Shugaban Iran Masoud Pezeshkian a ranar Asabar ya bayyana cewa ƙasar tasa ba za ta taɓa mika wuya ga Isra'ila da Amurka ba, yayin da yaƙin ya shiga mako na biyu.
Ya bayyana cewa, "dole ne ƙawayen Iran su tafi ƙabari da burinsu na ganin mutanen Iran sun miƙa wuya ba tare da sharadi," kamar yadda Pezeshkian ya bayyana, a cikin jawabin da aka watsa a gidan talabijin na ƙasar.
Isra'ila da Amurka sun kai farmaki kan Iran a ranar 28 ga Fabrairu inda suka kashe Jagoran Addini na Iran, Ali Khamenei inda hakan ya haddasa rikici a yankin.
Tun daga lokacin, Iran ta mayar da martani da harin makami masu linzami da jiragen sama marasa matuƙa a kan Isra'ila da wuraren Amurka a ƙasashen yankin na Gulf.
Pezeshkian na daga cikin mambobi uku na kwamitin shugabanci na wucin-gadi da ke jagorantar Iran tun bayan kisan Khamenei.
A lokacin jawabin, Pezeshkian ya nemi afuwa daga ƙasashen makwabta saboda hare-haren da Iran ta kai a faɗin yankin, yana mai cewa ba za a ci gaba da kai musu hare-hare ba sai dai idan hare-haren sun fito daga gare su.
"Dole ne na nemi afuwa a madadina da kuma a madadin Iran ga ƙasashen maƙwabta waɗanda Iran ta kai musu hari," in ji shi.
"Kwamitin shugabancin wucin-gadi ya yanke hukunci a jiya cewa ba za a sake kai hari kan ƙasashe makwabta ba kuma ba za a harba makami mai linzami ba sai dai idan harin da aka kai kan Iran ya fito daga wadancan ƙasashen," in ji shi.













