| Hausa
NIJERIYA
1 minti karatu
Nijeriya ta tara fiye da naira tiriliyan biyu daga harajin VAT a wata uku na karshen 2025 – NBS
Kuɗaɗen harajin VAT sun samu ne daga manyan sassa guda uku, harajin VAT na cikin gida, tiriliyan ₦1.12, da harajin VAT daga ƙasashen waje, biliyan ₦680, da harajin VAT na shigo da kaya biliyan ₦479.79 billion.
Nijeriya ta tara fiye da naira tiriliyan biyu daga harajin VAT a wata uku na karshen 2025 – NBS
NBS / Reuters
6 awanni baya

Hukumar Ƙididdiga ta Nijeriya, National Bureau of Statistics (NBS) ta sanar da cewa jimillar harajin VAT da ƙasar ta tatta a watanni uku na ƙarshen 2025 ya haura naira tiriliyan biyu.

Wani sabon rahoto daga NBS na ranar Talata, 3 ga Maris ya ce hukumar ta samu ƙari a harajin da take tattarawa da kashi 10.66%, idan aka kwatanta da watannin uku gabanin nan.

Harajin na VAT da aka tara ya ka naira tiriliyan ₦2.06 a watan Yuni zuwa Satumban 2025, yayin da na Oktoba zuwa Disamban 2025 ya koma naira tiriliyan 2.28.

Kuɗaɗen harajin VAT sun samu ne daga manyan sassa guda uku, harajin VAT na cikin gida, tiriliyan ₦1.12, da harajin VAT daga ƙasashen waje, biliyan ₦680.

Sai kuma harajin VAT na shigo da kaya daga ƙasashen waje, wanda ya kai biliyan ₦479.79.

Idan aka kwatanta da watanni uku na ƙarshen shekarar 2024 kuwa, harajin VAT ɗin da Nijeriya ta tattara ya ƙaru da kashi 28.10% cikin ɗari Q3 2024.