| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Iran ta ƙaddamar da harin makami mai linzami kan Isra'ila da sansanonin Amurka a ƙasashen Larabawa
Tehran ta ƙaddamar da harin ramuwar gayya kan sansanonin sojin Amurka a ƙasashen Bahrain da Qatar da UAE a daidai lokacin ake cikin fargaba bayan Isra’ila ta yi haɗin gwiwa da Amurka domin kai hari Iran a safiyar Asabar.
Iran ta ƙaddamar da harin makami mai linzami kan Isra'ila da sansanonin Amurka a ƙasashen Larabawa
Hare-haren ramuwar gayya na Iran sun biyo bayan hare-haren Isra'ila kan Tehran a safiyar Asabar / Reuters
12 awanni baya

Iran ta ƙaddamar da harin makami mai linzami na ramuwar gayya kan sansanonin sojin Amurka a fadin Gabas ta Tsakiya, inda aka ruwaito cewa harin da ya fi tasiri shi ne wanda ta kai kan hedkwatar Rundunar Sojan Ruwa ta 5 ta Amurka a Bahrain.

Kamfanin dillancin labaran Bahrain a ranar Asabar ya tabbatar da cewa wani makami ya sauka a cibiyar ayyukan Naval Support Activity Bahrain a yankin tashar jiragen ruwa na Juffair/Mina Salman.

"An kai harin makami kan cibiyar ayyukan Rundunar Sojan Ruwa ta Biyar. Za mu bayar da cikakkun bayanai daga baya," in ji Cibiyar Sadarwa ta Kasa ta Bahrain a cikin wata sanarwa.

Zuwa yanzu rundunar sojin Amurka reshen Gabas ta Tsakiya, ba ta fitar da wata sanarwa ba game da barna ko asarar rai.

Iran ta kai hari kan Isra'ila da makamai masu linzami, yayin da rahotanni ke cewa tsarin kariyar Isra'ila ya kakkaɓo su.

Sansanonin Amurka a Gabas Ta Tsakiya na fuskantar barazanar makami.

Wannan jerin harin makami an yi shi a matsayin martani kai tsaye ga harin da Isra'ila ta kai safiyar nan kan Tehran da wasu wuraren Iran, inda Amurka ta shiga cikin harin cikin gaggawa karkashin "Operation Epic Fury", a cewar sanarwar Ma'aikatar Tsaron Amurka.

Jami'an Iran sun sha gargadi sau da yawa cewa kowane hari a kan yankinsu zai haifar da ramuwar gayya kan sansanonin Amurka a ƙasashen makwabta.

Makamai masu linzamin Iran sun faɗa a wasu sansanonin Amurka a Gabas ta Tsakiya.

Hukumomin Qatar sun tabbatar da kakkaɓo makamai guda biyu masu linzami da suka nufo sararin samaniyarsu, inda babban sansanin jiragen saman Al Udeid — wanda a nan hedkwatar Rundunar Sama ta Amurka da ke Gabas ta Tsakiya take inda take da fiye da sojoji 10,00.

An ruwaito fashewa da hayaki a Abu Dhabi a Hadaddiyar Daular Larabawa, abin da ya sa aka rufe sararin samaniya nan take. A UAE sansanin Al Dhafra yake, wanda ke da muhimmanci ga rundunonin Amurka.

An kunna jiniya domin gargadi a birnin Amman, babban birnin Jordan, yayin da kafofin sada zumunta da rahotannin yankin ke ikirarin kai hare-hare kusa da sansanonin Amurka a can.

Kuwait da sauran kasashen Gulf da ke da sansanonin Amurka sun yi gargaɗi ‘yan ƙasashensu su zauna a wuraren da aka tanada masu bayar da kariya.