Babbar gasar ƙwallon ƙafa ta Mexico, Liga MX ta shiga ruɗani bayan da aka samu tashin hankali sakamokon kashe wani babban mai fataucin ƙwayoyi a ƙasar, wanda sojoji suka yi.
A yanzu an dakatar da wasannin da aka shirya bugawa a gasar, saboda rashin tsaro bayan da sojojin Mexico suka kashe jagoran CJNG, gamayyar masu safarar ƙwaya mafi girma a ƙasar.
Hukumar sojin Mexico ta tabbatar da kashe Nemesio Ruben Oseguera Cervantes, wanda shi ne jagoran Jalisco New Generation Cartel (CJNG).
Lamarin ya faru ne a wani yanki da ke da nisan awa biyu daga birnin Guadalajara, wanda yake cikin biranen da za su karɓi baƙuncin gasar Kofin Duniya na 2026.
Kisan da aka yi wa gawurtaccen mai safarar ta haddasa damuwa game da amincin al’ummar rayuwa a yankuna da johihi da dama a Mexico.
Harin sojin ya faru ne a Tapalpa, Jalisco, wanda ya janyo aka ɗage wasannin ranar Lahadi, guda huɗu na gasannin daban-daban.
Tashin hankali ya hana tafiye-tafiye
Ƙungiyar ta CJNG ita ce ƙungiyar masu manyan laifuka mafi girma da ƙarfin iko a Mexico, inda aka ƙiyasta tana da mambobi 19,000, kuma tana da rassa a jihohi 21 cikin 32 na ƙasar.
Kamar yadda aka tsammata, kisan ya haifar da harin ramuwa a faɗin yankin. An samu rahotannin ƙone-ƙonen motoci da toshe manyan hanyoyi a ƙasar wanda mambobin ƙungiyar suka yi.
Wannan tashin tashina ta haifar da tasgaro a harkokin jigila da hada-hadar mutane, da ‘yanwasa da masoya. Wannan salon ta da hankali wata dabara ce da ƙungiyoyin ta’adda ke bi a yankin.
Suna hakan ne da fatan hana tafiyar jami’an tsaro, sai dai kuma abin yakan haifar da dagula hada-hadar jama’a da al’amuran sufuri. Amma duk da haka, wasu al’amuran wasanni suna ci gaba da gudana kamar yadda aka tsara.
Wasannin tanis na Mexican Open, na ATP tennis sun gudana a Acapulco, Guerrero, kuma ana sa ran za su ci gaba ranar Litinin.
Gasar Kofin Duniya
Mabiya harkokin ƙwallo a duniya na lura da abin da ke faruwa a Mexico, saboda tana ɗaya daga cikin ƙasashe uku da a nan ne za a buga gasar kofin duniya ta FIFA 2026.
Hukumomin ƙwallo suna fifita amincin ‘yanwasa da ‘yankallo sama da jadawalin wasa. Wannan na nufin za a iya cewa batun kofin duniya a Mexico ya shiga fargaba.
Filin wasa na Guadalajara yanzu zai zama abin tantama ga mahukunta a FIFA, saboda ana tsara buga wasanni huɗu cikinsa a gasar da za ta gudana a watan Yuni.
Daga ƙasashen da za su buga wasa a Guadalajara akwai Korea ta Kudu, Sifaniya, Uruguay, da Colombia, da kuma mai masaukin baƙi Mexico.







