| Hausa
WASANNI
1 minti karatu
Bukayo Saka ya zama ɗanwasan Arsenal mafi yawan albashi a tarihi
Matashin ɗanwasan Arsenal, Bukayo Saka ya sanya hannu kan sabuwar kwantiragi, kuma ya zama ɗanwasan da ya fi kowa ɗaukar albashi a tarihin Arsenal.
Bukayo Saka ya zama ɗanwasan Arsenal mafi yawan albashi a tarihi
Bukayo Saka ɗan asalin Ingila ne tsatson Nijeriya mai shekaru 24. / Reuters
5 awanni baya

Matashin ɗanwasan Arsenal, Bukayo Saka ya rattaba hannu kan sabuwar kwantiragi da za ta haura tsohuwar kwantiraginsa da aka shirya za ta ƙare a 2027. Sa hannun ya mayar da shi mai albashi mafi tsoka a tarihin ƙungiyar.

Tun a farkon shekarar nan ne ɗanwasan ɗan asalin Ingila ya amince da ci gaba da zama ƙungiyar, amma sai a yanzu ya sanya alƙalami a takarda kan kwantiragin da za ta kai 2031.

Mai shekaru 24, Saka ɗan wasa ne mai tsatson Nijeriya kuma yana da farin jini wajen masoya Arsenal. A yanzu ya tsawaita zamansa da shekaru biyar.

Sabuwar kwantiragin za ta ba shi albashin da ya haura fam £300,000 duk mako.

Bukayo Saka ya bi sahun ‘yanwasan Arsenal da suka tsawaita zamansu a ƙungiyar cikin watannin baya-bayan nan, irinsu William Saliba, Gabriel, Ethan Nwaneri, da Myles Lewis.

A kakar bana, Saka ya ci ƙwallaye bakwai cikin wasanni 33 a duka gasanni, kuma yana cikin zaratan ‘yanwasan da koci Mikel Arteta ke ji da su a tawagarsa a ‘yan shekarun nan.