| Hausa
NIJERIYA
3 minti karatu
Nijeriya ta gargaɗi ‘yan ƙasar kan faɗawa tarkon masu ɗaukar ma’aikata su tura su wurin yaƙi
Ma’aikatar Harkokin Wajen Nijeriya ta nuna damuwarta kan yadda ake yaudarar jama'a da ayyuka masu albashi mai tsoka da damar karatu ko kuma sauƙin samun izinin zama, amma daga baya a tura su wuraren yaƙi.
Nijeriya ta gargaɗi ‘yan ƙasar kan faɗawa tarkon masu ɗaukar ma’aikata su tura su wurin yaƙi
Rahotanni sun ce an yaudari 'yan ƙasashen Afirka da dama inda aka kai su wuraren yaƙi a matsayin sojojin haya / Others
10 awanni baya

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta gargaɗi ‘yan ƙasar da su guji faɗawa tarkon masu ɗaukar ma’aikata ba bisa ƙa’ida ba da ke yaudarar jama’a domin tura su shiga yaƙe-yaƙe na makamai a ƙasashen waje.

A cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Waje ta fitar a ranar Lahadi a Abuja, gwamnatin ƙasar ta bayyana matuƙar damuwarta kan ƙaruwar al’amuran da ake samu na yaudarar ’yan Nijeriya tare da ɗaukarsu aiki bisa ta hanyar yaudara.

A cewar ma’aikatar, an yi wa wasu alƙawarin ayyuka masu albashi mai tsoka da ayyukan tsaro da damar karatu ko kuma sauƙin samun izinin zama, amma daga baya a tura su wuraren yaƙi bayan an tilasta musu rattaɓa hannu kan kwantiragin aikin soja.

Gwamnatin ta ce rahotanni sun nuna cewa masu ɗaukar ma’aikatan kan yi amfani da tayin albashi mai yawa a kowane wata, kuɗin shiga aiki, da kuma alƙawarin samun zama ɗan ƙasa cikin sauri domin jan hankalin mutane.

A wasu lokuta, an ce an tilasta wa waɗanda abin ya shafa sanya hannu kan takardu a cikin harshen waje ba tare da samun shawarwarin lauya ba, sannan a kwace takardun tafiyarsu bayan sun isa ƙasar. Ma’aikatar ta kuma nuna yiwuwar hannun masu shiga tsakani da ke shirya tafiya ta hanyar bizar yawon shakatawa ko wasu nau’ikan biza da ba na soja ba.

Gwamnatin Tarayya ta yi gargaɗin cewa shiga rikice-rikicen makamai a ƙasashen waje ba tare da amincewar gwamnati ba na iya saɓa wa dokokin Nijeriya da na ƙasa da ƙasa kan batun shiga aikin sojan haya da shiga rundunar wata ƙasa. Ta jaddada cewa irin wannan mataki na iya jefa rayuka cikin haɗari tare da haifar da manyan matsalolin shari’a.

Domin magance lamarin, gwamnati ta ce tana aiki tare da abokan hulɗa na cikin gida da na ƙasa da ƙasa domin bincike da kuma wayar da kan jama’a kan illolin wannan ɗaukar ma’aikata ta haramtacciyar hanya. Haka kuma an umarci ofisoshin jakadancin Nijeriya a ƙasashen waje su ƙara sa ido tare da bayar da shawarwari cikin gaggawa ga ’yan Nijeriya.

Ma’aikatar ta roƙi iyaye da masu kula da yara da shugabannin al’umma da cibiyoyin ilimi su wayar da kan matasa kan haɗarin irin waɗannan dabarun yaudara. Ta kuma shawarci ’yan ƙasa su tabbatar da duk wani tayin aiki ko karatu a ƙasashen waje ta hanyoyin hukuma, tare da kai rahoton duk wani abin da ya yi kama da zamba ga hukumomin da suka dace.