Jami’an Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Nijeriya (NDLEA) sun daƙile wani yunƙuri na ban mamaki da masu fataucin miyagun ƙwayoyi biyu suka yi na safarar hodar Iblis da miyagun ƙwayoyi da suka ɓoye a cikinsu, da kuma wata mata da ta yi cikin bogi inda ta ɓoye ƙwayoyin a ciki.
An kama ɗaya daga ciki a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano da ke Kano, ɗaya kuma a kan iyakar Seme da ke Legas domin tsallakawa zuwa Turai da wasu wuraren.
A ranar Litinin 16 ga Fabrairu, jami’an NDLEA sun kama wata mata ‘yar kasuwa da ke zaune a Kano mai suna Rabi Muhammad mai shekara 35 a kan iyakar Seme a yunƙurinta na shiga Cotonou.
Bayan jami’an na NDLEA sun gama caje ta, sai suka gano ta kifa ƙwarya a cikinta domin yin cikin bogi, inda ta naɗe cikin da ƙyalle mai ruwan hoda kamar yadda wani bidiyo da hukumar ta NDLEA ta wallafa ya nuna.
Hukumar NDLEA ɗin ta ce matar ta ɓoye kafso 3,200 na ƙwayar Tramadol a cikin ƙwaryar wadda take da niyyar kaiwa Cotonou domin ta sayar.
A wannan rana a Kano, Jami’an NDLEA a wurin tantance fasinjoji na filin jirgin Malam Aminu Kano sun kama wani ɗan ƙasar Ivory Coast mai shekaru 41 mai suna Michael Gohouri (wanda aka fi sani da Anunwa Onyinye Michael), yayin duba fasinjojin jirgin Ethiopian mai lamba ET940 zuwa Milan Malpensa ta Addis Ababa.
Hukumar NDLEA ta ce a lokacin da aka kai shi gaban na’ura domin duba jikinsa, sakamakon ya tabbatar da cewa ya haɗiye miyagun ƙwayoyi.
Bayan haka, an tsare shi domin sa ido, inda daga bisani ya fitar da kunshe-kunshe 82 na hodar Iblis da nauyinsu ya kai kilo 1.49. Michael Gohouri ya isa Legas daga Milan a ranar 17 ga Janairun, 2026, kuma ya riƙa zirga-zirga tsakanin Legas da Enugu na tsawon makonni uku.
Daga bisani ya tafi Kano inda ya kwashe mako guda kafin ya haɗiye ƙwayoyin hodar Iblis a ɗakin otal ɗinsa inda aka yi alƙawarin ba shi Euro 5,000 idan ya kai kayan zuwa Milan.














