NLC ta ci gaba da yajin aikin a kwana na biyu duk da tattaunawarsu da gwamnatin Nijeriya.

An shiga rana ta biyu ta yajin aiki a faɗin Nijeriya, inda ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC suka dakatar da hada-hada da duk wasu al'amura a faɗin ƙasar, ciki har da rufe asibitoci da bankuna da sauka da tashin jirage.

Sai dai a ranar farko ta fara yajin aikin wato Litinin da daddare, wakilan gwamnatin tarayya da na ƙungiyoyin ƙwadagon sun yi wata ganawa wacce aka cimma matsaya huɗu, amma duk da haka NLC ba ta sanar da janye yajin aikin ba.

A takardar yarjejeniyar da TRT Afrika ta gani wacce wakilan gwamnati biyu Ministocin Watsa Labarai da na Ƙwadago Mohammed Idris da Nkeiruka Onyejeocha da kuma wakilan ƙwadago shugabannin NLC da TUC Joe Ajaero da Festus Osifo suka sanya wa hannu, an cimma matsaya huɗu.

Takardar ta ce: "A ranar Litinin 3 ga watan Yuni ne gwamnatin tarayya ta kira wani taro da kungiyar kwadago a ofishin sakataren gwamnatin tarayya, da nufin kawo karshen yajin aikin. Bayan gamammiyar shawara.

"Bayan tattaunawa da tuntubar juna daga bangarorin biyu, an cimma matsaya kamar haka:

1. Shugaban kasa, Babban Kwamandan Askarawan Nijeriya, ya ƙuduri aniyar biyan mafi ƙarancin albashi wanda ya haura N60,000.

2. Dangane da abin da ke sama, kwamitin ɓangarori uku zai gana a kowace rana har tsawon mako guda da nufin cimma matsaya kan mafi ƙarancin albashi na ƙasa;

3. 'Yan ƙwadago bisa mutunta girman Shugaban Ƙasa da jajircewar gwamnatin tarayyar Nijeriya la'akari da mataki na biyu na sama, ta dauki nauyin gudanar da taron ganawa da tattaunawa da dukkan rassa da ɓangarorinta don jin amincewarsu a kan matakan

4. Ba za a ci mutunci ko zarafin kowane ma'aikaci ba saboda wannan yajin aikin.

Tasirin yajin aikin a ranar farko

Tun da fari a ranar Litinin gwamnatin Shugaba Tinubu ta nemi 'yan ƙwadago da su janye yajin aikin su koma bakin tattaunawa, bayan da ganawar da shugaban majalisar dattawan Nijeriya Godswill Akpabio da takwaransa na majalisar wakilai Tajedeed Abbas suka yi da wakilan 'yan ƙwadagon ranar Lahadi ta gaza shawo kan yunƙurin shiga yajin aikin.

Yajin aikin ya janyo durƙushewar al'amura da dama da suka shafi mutane kai tsaye, musamman na katse babban layin wutar lantarki na Nijeriya da NLC ta yi, kamar yadda kamfanin da ke rarraba hasken lantarki na ƙasar (TCN) ya faɗa.

Kazalika yajin aikin da ƙungiyoyin ƙwadago ke yi a ya kawo cikas a filin jirgin saman ƙasa da ƙasa na Murtala Muhammed da ke Lagos, babban birnin kasuwanci.

A jihar Kano da ke arewacin ƙasar, 'yan ƙungiyar sun rufe makarantu da ma'aikatu da bankuna har ma da kotuna a yunƙurinsu na tabbatar da tasirin yajin aikin.

Su dai gamayyar ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC suna so ne gwamnatin Bola Tinubu ta riƙa biyan ma'aikata aƙalla N497,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi.

TRT Afrika