Daga
Charles Mgbolu
Yanzu karfe 8:30 ne na safiyar ranar Litinin a babbar kasuwar Ogbete a jihar Enugu da ke Kudu maso Gabashin Nijeriya.
Chinonso (wanda ba sunansa na ainihi ba ne) ya tsaya a gaban shagonsa wanda yake sayar da tufafin zamani a wani layi jere da shaguna, yana cikin kokwanton yadda ranar za ta kasance.
Ya dauki lokaci yayin bude shagon, ya waiga yana kallo ko akwai wani da zai dauki hankalinsa. Idonsa na kallon duk wani mutum da ke wucewa, yana kokarin fahimtar su waye kuma me abin da za su yi.
Za ka kwashe lokaci kafin ka fahimci abin da Chinonso yake yi – yana so ya tabbatar da cewa babu wata matsala, sai ya bude shagonsa.
Abin da Chinonso da sauran 'yan kasuwa suke yi kenan kowace ranar Litinin a wannan kasuwa. Suna tafiyar da harkokin kasuwancinsu ne a ankare a 'yan makonnin nan, inda suke bijire wa al'adar nan ta zaman gida da ake yi kowace ranar Litinin.
An fara wannan al'adar ne a watan Agustan 2021, wadda kungiyar masu fafutikar kafa kasar Biyafara (IPOB) ta kirkiro kuma wani bangare ne na nuna adawa da ci gaba da tsarewa da kuma yi wa jagoransu Nnamdi Kanu shari'a.
Yayin da kungiyar IPOB ta yi watsi da zanga-zangar bayan mazauna gari sun ce dokar tana shafar rayuwarsu, wani bangare na mayakan kungiyar — da ake kira "'yan bindigar da ba a san ko su waye ba, masu dauke da makamai" — sun ci gaba da jaddada dokar zama a gida da karfin tsiya.
Yadda suke jaddada dokar ya hada da harbin kan mai uwa da wabi da satar mutane da cinnawa gine-gine wuta da fasa gidan yari da kashe-kashe.
Wadanda harin ke rutsa wa da su sun hada da mazauna yankin da 'yan kasuwa da 'yan siyasa da cibiyoyin gwamnati da kuma duk wani wanda ra'ayinsa ya bambanta da nasu a birane ko kuma a karkara.
'Yan kungiyar ne suke da alhakin ta'asar da aka yi wa daruruwan mutane da jami'an tsaro, inda suke sanya tsoro a zukatan jama'a a yankin.
Kusan shekara biyu kenan wani bangare mai girma na yankin kudu maso gabashin Nijeriya ya kasance tsit a ranar Litinin saboda tsoron hare-hare daga 'yan bindiga wadanda suke jawo a kan tituna.
Wani abu ya faru a ranar 28 ga watan Yuni a Enugu, inda daruruwan mazauna garin suka hau kan tituna a wata zanga-zangar lumana, suna cewa a harshen Turancin Pidgin, "Our mumu don do (our eyes are now open)", wato suna cewa ne rashin wayonmu ya isa haka (idonmu ya bude yanzu).
Ta fuskoki da dama hakan yana nuna yadda mutane suka fara samun 'yanci daga kangin bauta na wasu 'yan bindiga da ba a san su ba wadanda suke rufe su a gida kowace ranar Litinin kusan shekara biyu kenan.
Chinonso, wanda shi ma ya shiga gangamin, ya ce ya gaji da wannan koma bayan a rayuwarsa da kasuwancinsa.
"Ranar 3 ga watan Juli ita ce rana ta farko da na bude shagona a ranar Litinin ba tare da jin tsoro ba tun shekarar 2021," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika. "Har tsawon wane lokaci ne za mu ci gaba da wannan?"
Karuwar asarar rayuka
A watan Disambar 2021, Cibiyar Rajin Kyautata Ayyukan Majalisun Dokoki da Yaƙi da Rashawa a Najeriyar wato CISLAC ta ce an kashe mutum 150 a watanni biyar na farko tun da aka fara dokar zama a gida a jihohi biyar na yankin.
Jihar Ebonyi inda aka kashe mutum 101 ita ce ta fi yawan wadanda suka rasa rayukansu, daga ita sai jihar Imo inda aka kashe mutum 60.
A Anambra mutum 37 aka kashe, yayin jihar Abiya ta rasa mutum 33. Sai mutum 22 da aka kashe a jihar Enugu, kamar yadda cibiyar CISLAC ta bayyana.
Jami'an tsaro a Nijeriya sun kaddamar da hare-hare a kan kungiyar, inda aka kashe kuma aka kama wasu mambobin kungiyar. Amma daga nan toshe wata kafa da kungiyar ke amfani da ita, sai kungiyar ta kara huda wata sabuwar kafa.
Tasirin aikace-aikacen kungiyar ya shafi tattalin arzikin jihohin kudu maso gabashin Nijeriya.
Farfesa Charles Soludu shi ne gwamnan jihar Anambra kuma tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya ce yankin ya yi asarar naira biliyan 19.6 (dala miliyan 25.3) zuwa watan Disambar 2022, bayan an kwashe shekara daya na tilasta rufe kasuwanci a kowane farkon mako.
Yayin da aka fara dawo daga rakiyarsu, Chinonso ya ce akwai mutane da yawa da ke jin tsoro har yanzu.
"Tsoron harin mayar da martani shi ne matsalar. Ba a harkokin kasuwanci sosai a ranar Litinin saboda mutane kadan ne suke zuwa kasuwanni. Wadanda suka fito kuma ba sa yin nisa. Suna sayan muhimman abubuwan da suke bukata ne. Da wuya ka ga mutane suna barin gidadensu ranar Litinin, misali, don su sayı kayan sawa," in ji shi.
Sai al'umma ta tashi tsaye
Masu sharhi kan tsaro sun ce ya kamata a jinjina wa wadanda suka kalubalanci dokar zama gida ta 'yan awaren IPOB.
"A gaskiya ina jin tsoron cewa 'yan bindigar za su iya daukar mataki," in ji Dokta Kabiru Adamu masani kan harkokin tsaro. Babu tabbas, kuma a nan ne ya kamata gwamnati ta shigo don tabbatar da cewa hakan bai faru ba. Ya kamata a samar da ingantaccen tsaro ga mutane wadanda suka nuna kwarin gwiwa saboda kada a yi asarar kokarinsu."
Gwamnonin jihohin yankin kudu maso gabashi sun yi alkawarin samar da tsaro kuma sun bukaci jama'a su fito ranar Litinin don gudanar da al'amuransu.
Wannan ya zama kalubale ga 'yan kasuwa wadanda ba sa fitowa ranar Litinin. Ana musu kallon masu goyon bayan haramtacciyar dokar zama a gida, kuma gwamnati za ta iya dirar musu.
A jihar Enugu, akwai dokar da ta tanadi a rufe shaguna ko wuraren kasuwancin da ba sa fitowa ranar Litinin.
"Ba na ganin hakan mataki ne da ya dace. Hakan ya jawo arangama tsakanin 'yan kasuwa da jami'an tsaro a wannan kasuwa, kuma ba na ganin wannan ne abin da ya kamata gwamnati ta mayar da hankali a kai.
"Ya kamata ne gwamnati ta samar da tsaro wadda hanya ce da za ta sa mutane su sake aminta da gwamnati," in ji Chinonso.
"Da zarar mutane suka ga cewa an samar musu da wadataccen tsaro, da kansu za su dawo da ci gaba da harkokin kasuwancinsu a ranar Litinin."
Haka zalika Kabiru Adamu ma ya goyi bayan hakan. "Ya kamata gwamnati ta sake tunani. Bai kamata su hukunta mutane saboda suna jin tsoron 'yan bindiga, wadanda an san cewa suna kai wa mutane hari a fili kuma su kashe wadanda suka yi biris da dokarsu ta zama a gida," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.
"Yanzu tun da mutane ba san jin wani sauran tsoro, wannan babbar dama ce da gwamnati za ta iya yin amfani da ita wajen yakar 'yan bindigar."