Hedkwatar Tsaron Nijeriya ta ce wata sabuwar ƙungiyar ta'addanci mai suna Lakurawa ta ɓulla a arewa maso yammacin ƙasar.
Daraktan Watsa Labarai na Hedkwatar TSaron Manjo Janar Edward Buba ne ya shaida wa manema labarai hakan a yayin da yake jawabi kan ayyukan rundunar tsaron a ranar Alhamis a Abuja.
Ya bayyana cewa sabuwar ƙungiyar ta samo asali ne daga Jamhuiryar Nijar bayan juyin mulkin da aka yi, wanda ya damalmala haɗin kan soji da ke tsakanin Nijeriya da Nijar.
Manjo Janar Buba ya ce 'yan ta'addan sun fara shiga yankunan arewacin jihohin Sokoto da Kebbi ne daga Jamhuriyar Nijar da Mali, musamman bayan faruwar juyin mulkin Nijar ɗin.
Ya ce a baya can ayyukan hadin kai na soji da ke tsakanin dakarun Nijar da Nijeriya kafin juyin mulkin su suka hana ƙungiyar rawar gaban hantsi.
Mai magana da yawun rundunar tsaron ya ƙara da cewa, "'Yan ta'addan sun yi amfani da damar giɓin da aka samu na haɗin kai tsakanin ƙasashen biyu suka shiga yankunan jihohin don su yaɗa aƙidunsu.
Manjo Janar Buba ya tabbatar da cewa dakaru sun samu bayanan sirri kuma suna ƙoƙrin daƙile 'yan ta'addan.
Tuni 'yan ƙungiyar suna ci gaba da samun mafaka a yankuna da dama da uzzura wa mazaunan wuraren, amma dakaru na ta ƙoƙarin kawar da su ba dare ba rana, in ji shi.