Shin lokaci ya yi na a hana amfani da sinadarin dake kashe yaran Gambiya?

Mutuwar yara kanana a kalla 69 a Gambiya bayan shan maganin tari gurbatacce, ya harzuka masana kiwon lafiya na duniya.

Yaran na da shekaru kasa da biyar, kuma mafi yawansu ma jarirai ne. A duniya, iyaye na ywan sayen magunguna a shaguna kawai, a lokacin da yaransu suke zazzabi, tari ko kumburin makogoro.

Likitoci sun daina bayar da shawarar amfani da maganin tari na ruwa, bayan da suka gano ba sa taimakawa wajen maganin tari ko zazzabi ga yara kanana.

“A aiyukana, ba na rubutawa marasa lafiya maganin tari na ruwa. Magana ta gaskiya, ba a gano cewa amfani da maganin tari na ruwa na taimakawa yara kanana samun waraka daga tarin ba. Muna bayar da shawarar amfani da zuma da lemon tsami.”, inji Emmanuel Agogo, Likita dan Najeriya.

Ya fadawa TRT World cewa “Wadannan magunguna na ruwa ba sa warkar da yara daga tarin”.

Gambiya, kasar Afirka matalauciya dake da mutane miliyan 2.4, ba ta da kamfanunnukan magunguna. Ana sayo magungunan ruwan daga kamfanin Indiya mai suna Maiden Pharmaceuticals, wanda a kwanakin nan ya fuskanci bincike game da ingancin magungunansa.

A ranar 5 ga Oktoba, WHO ta bayar da gargadi ga duniya kan gurbatattun magungunan yara kanana.

Magugunan ruwan guda hudu --- Promethazine Oral Solution, Kofexmalin Baby Cough Syrup, Makoff Baby Cough Syrup da Magrip N Cold Syrup, duk an gano suna dauke da sinadarin diethylene glycol (DEG).

Dr. Peter Adebayo Adewuyi, Mai Bayar da Shawara Kan Horo Game da Cututtuka a Gambiya ya bayyana cewa “Daga gwaje-gwajen da aka yi a nan, an gano akwai kaso 19 na wannan sinadari a cikin magungunan, wanda kamata ya yi kar ya wuce kaso 0.1.”

Ya fadawa TRT World cewa “Wannan adadi ya ninninka yadda ya kamata a ce an samu a cikin magungunan.”

Kusan karni guda, DEG – wani sinadari mai zaki da suke samarwa, na zama mai guba idan aka gauraya shi da magunguna. A mafi ywanci, kamar yadda ya faru a Gambiya, mutanen da suke shan DRG na gamuwa da ciwon koda, kuma su mutu cikin kankanin lokaci.

Duk da haka, wannan sinadari ya shiga cikin magunguna da dama a kasashe irin su Bangaladsh da Haiti, tare da kashe mutane da yawa a kasashen.

An kafa Hukumar Kula da Kayan Abinci da Magunguna (FDA), hukumar Amurka wadda gwamnatoci suke aiki da shawarwarin da ta bayar kan amfani da magunguna, saboda samun amfani da DEG a 1930.

Mafita daga rasa rayuka

A shekarar 1037 ne aka fara samun rasa rayuka da dama sakamakon amfani da magungunan DEG a Amurka.

Wani baganin ruwa da ake kira Elixir of Sulfanilamide, ya fita kasuwa ba tare da an yi gwajin sa ba. Kusan mutane 105 da suka hada da yara kanana 34 sun mutu cikin ‘yan kwanaki kadan bayan shan maganin.

Kuka da korafin da aka yi ta yigame da maganin ne ya sanya gwamnatin Amurka talokacin ta kafa Hukumar Kula da Kayan Abinci, Kayan Kwalliya da Magunguna ta Tarayya krkashin dokar 1938, wadda ta baiwa wannan hukuma ikon tantance kayan abinci da magunguna kafin a fara sayar da su.

Tun wannan lokaci an ci gaba da samun rasa rayuka sakamakon amfani da magungunan DEG a sassan duniya.

Ana yawan amfani da DEG ne wajen samar da sinadaran kamfanunnuka da ababan hawa irin su man birki, tawada da sauran su.

Wasu kamfanunnukan magunguna sun yi kuskure wajen gauraya DEG a matsayin sirki ga magunguna don rage kudaden da za su kashe maimakon sayen glycerine ko polyethene glycol wadanda suke da tsada sosai.

Dr. Joel Selanikio, kwararre dake aiki da WHO ya shaidawa TRT World cewa “Bata gari za su iya cin riba da yawa su yi amfani da DEG, suna kuma sayar da shi da sunan PEG ko glycerine.”

A shekarar 2006 sama da mutane 100 ne suk mutu a Panama sakamakon amfani da magungunan da suke dauke da Deg da yawa (AP).

Ana sayar da magungunan na ruwa ta ci barkatar a dakaunan shan magani.

“ba ma iya shawo kan lamarin duba da yadda ake shan wahalar samun kula da lafiya da kuma yadda wuraren sayar da magunguna nan ne wajen farko da mutane ke fara zuwa idan ba sa jin dadi. Wadannan mutane ne ke rubuta magunguna.” Inji Agogo, wanda ya samu zama kwararre kan ACDC Kofi Anan 2021.

Gwamnatin Indiya ta tabbatar da cewa an samar da wannan magani gurbatacce ga kasar Gambiya kawai. Amma WHO ta yi gargadin cewa akwai yiwuwar an yi fataucin wasu kwalaben maganin zuwa wasu kasashen.

Raunin tantancewa

Masu sana’ar sayar da magunguna na Haryana, sun bayyana cewa mutuwar da aka samu a Gambiya ba bakon abu ba ne ga hatsaniya.

An dakatar da kamfanin tare da cin sa tara a wata jiha ta Indiya da ake kira Bihar sakamakon sayar da magunguna marasa inganci. Yana daga cikin kamfanunnuka 39 dake samar da magunguna da kasar Vietnam ta sa masa jan fenti, inji jaridar Times of India.

A lokacin da Kungiyar Masu samar da magugunan ke fadin “Abun da ban ta’ajibi” game da lamarin, mahukuntan Indiya tare da WHO suna bincike kan yadda aka zuba sinadarin DEG mai guba a cikin maganunnunan na ruwa.

Dr. Selanikio ya shaida cewa “Amfani da kayan bincike da tantancewa masu kyau irin su ‘mass spectroscopy ‘ za su iya gano wata guba ko DEG da aka zuba a cikin wani magani nan take.”

“Babu wani kamfani da ya san abunda yake yi da zai yi amfani da DEG yana sane, ko glycerine da ya gurbata da DEG. Idan aka samu sun yi amfani da DEG da yawa, to dole akwai sakaci: rashin kyakkawar kulawa da tantancewa saboda gaza gano DGE din.”

Mafi yawanci sakaci ne daga kamfanunnukan da ake samar da magungunan yke janye samuwar DGE a cikinsu, maimakon amfani da gurbatatte cikin sani.

Mahukuntan Gambiya na fuskantar suka kan me ya hana su fara gwajin maganin akafin fara sayar da shi a kasuwanni.

Duk da yunkuri a lokuta daban-daban, Markieu Janneh Kaira, Daraktar Hukumar Kula da Kayan Abinci da Magunguna ta Gambiya ba ta iya kula TRT World ba.

Gambiya ba ta da dakin bincike na kanta da za ta iya auna inganci ko akasan haka na magungunan.

Dr. Adewuyi ya ce “Ko ma mene ne, ba zai yiwu a ce za a auna ingancin kowanne magani da aka shigo da shi ba. Ko Amurka ba ta da ikon yin hakan.”

TRT World