Hedikwatar Tsaron Nijeriya ta ja hankalin ‘yan ƙasar da suke yaɗa hotunan wani babban jami’in sojanta Birgediya Janar MS Adamu bisa zarginsa da hannu a matsalar wani sojan ruwa Seaman Abbas Haruna da labarin tsare shi ya yaɗu kamar wutar daji.
A ƙarshen makon da ya gabata ne matar Seaman Abbas ta bayyana a wani shirin talabijin na Brekete Family tana zargin wani babban soja mai suna Birgediya Janar MS Adamu da tsare mijinta tsawon shekaru shida.
Sai dai sanarwar da Hedikwatar Tsaron ta fitar a yau Talata mai ɗauke da sa hannun darakta janar na sashen watsa labaranta, Birgediya Janar Tukur Gusau ta ce hotunan Birgediya Janar Adamu da ake ta yaɗawa a shafukan sada zumunta ba shi da hannu a lamarin Seaman Abbas.
“A don haka, Hedikwatar Tsaro na son amfani da wannan damar wajen kira ga ‘yan ƙasa da su bar kwamitin da Babban Hafsan Tsaro na Ƙasa Janar Christopher Gwabin Musa ya kafa ya kammala bincikensa ba tare da nuna ƙyama ga ra’ayoyin jama’a ba,” in ji sanarwar.
Kazalika Hedikwatar Tsaron ta roƙi jama’a da su guji yin magana a kan ƙarya wacce za ta iya keta haƙƙin ɗan’adam da kutse cikin rayuwar babban jami'in.
Sanarwar ta ce “Babban sojan na da damar neman shigar da ƙarar duk wani mutum ko wata ƙungiya da ta wallafa hotonsa tana alaƙanta shi da lamarin Seaman Abbas.”
Hedikwatar Tsaron ta kuma ce hukumomin soji na ci gaba da bai wa ‘yan Nijeriya tabbacin tabbatar da bin doka da oda. “Za mu yi duk mai yiyuwa don mu kai ga kawo karshen lamarin, kuma za a sanar da jama’a yadda sakamakon ya kaya.”