Hatsarin kwale-kwale ya rutsa da akalla mutum 40 daga kauyen Kasabu wanda ke Karamar Hukumar Agwara na Jihar Neja.
Kwale-kwalen ya yi hatsari ne a lokacin da yake hanyar zuwa Yauri da ke Jihar Kebbi.
Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya ya ruwaito Darakta Janar na Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja, Salihu Garba na cewa lamarin ya faru ne a ranar Litinin tsakanin 11 na safe zuwa 12 na rana.
Ya bayyana cewa wani wanda ya tsira daga hatsarin ya shaida cewa kwale-kwalen na dauke da akalla mutum 22.
Sai dai a ranar Talata Bala Mohammad wanda shi ne shugaban gudanarwa na gundumar Yauri ya bayyana cewa "Har yanzu muna neman fasinjoji 40 da taimakon masu aikin ceto na ruwa wadanda".
Ya bayyana cewa ma’aikatan agaji da masu kwale-kwale na ci gaba da neman wadanda suka tsira domin ceto su.
Haka kuma ya kara da cewa babu wani fasinjan da aka gano zuwa yanzu.
Daraktan ya ce ana zaton cewa igiyar ruwa ce ta jawo kwale-kwalen ya kife da mutanen.
Ana yawan samun hatsarin jirgin ruwa a Nijeriya musamman a lokacin damina.
Ko a watan da ya gabata sai da gomman mutane suka rasu sakamakon kifiwar kwale-kwale a Nijeriya.