Yajin aikin da ma'aikata ke yi a fadin Nijeriya ya gurgunta harkokin tattalin arziki a kasar a daidai lokacin da take fama da hauhawar farashin kayayyaki.
Kungiyoyin Kwadago na NLC da TUC ne suka ayyana tafiya yajin aikin tun tsakar daren Talatar da ta wuce, sakamakon wata takaddama tsakaninsu da gwamnatin jihar Imo kan zargin cin zarafin shugaban NLC da 'yan sandan jihar suka yi, mako biyu da suka wuce.
Duk da cewa gwamnatin tarayya ta gana da shugabannin kungiyoyin ƙwadagon a ranar Laraba, ba a cimma wata ƙwaƙƙwarar matsaya don janye yajin aikin ba.
Shugaban ƙungiyar ƙwadago ta ƴan kasuwa TUC, Festus Osifo ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa nan gaba kadan kungiyoyin kwadagon za su shiga wani yajin aikin na sai baba ta gani, don neman gwamnati ta cika yarjejeniya kan matakan da za a dauka na magance tsadar sufuri da abinci da magunguna, bayan cire tallafin man fetur.
"Baya ga gazawar gwamnati wajen aiwatar da yarjejeniyarmu, muna kuma neman ta zaƙulo waɗanda suka ci zarafin shugaban NLC tare da gurfanar da su a gaban shari'a.
Shugaban NLC ya je Jihar Imo ne don warware batun rashin biyan albashin ma'aikata da sauran hakkokinsu, amma sai aka ci zarafinsa, kuma ƴan sanda suka yi masa duka da ma wasu abubuwa da aka alaƙanta da gwamnatin jihar," in ji Osifo.
Durkushewar al'amura
Yajin aikin ya durƙusar da ayyukan bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kuɗaɗe da na tasoshin jiragen ruwa da fannin layin dogo da fannin man fetur da ma dakatar da karatu a wasu makarantun gwamnati a wasu sassan ƙasar duk a ranar Laraba, kwana na biyu da fara yajin aiki.
A makarantu irin Jami'ar Bayero ta Kano har soke yin jarrabawar zangon karatu na farko da ɗalibai ke zanawa aka yi a ranar Laraba.
Lamarin ya kuma jawo ɗaukewar wutar lantarki na baki dayan yinin Laraba a Nijeriyar, inda hakan ya zamo wa mutane da dama, musamman masu harkokin kasuwanci asara.
Masu sharhi irin su Musa Njadvara, wani wakilin jaridar The Guardian ta Birtaniya a kan tattalin arziki, ya ce lamarin zai durƙusar da ƙasar, wadda ita ce mafi ƙarfin tattalin arziki a Afirka.
"Yajin aikin zai ci gaba da yin illa ga tattalin arzikin ƙasar da dama ke cikin matsala.
"Hakan zai kara ta'azzara hauhawar farashin kayayyakin da ake fama da ita saboda hada-hada za ta ragu a yayin da buƙatar kayayyaki kuma za ta ƙaru.
Nijeriya za ta yi asarar ƙarin kuɗaɗe. Hakan zai shafi darajar tattalin arzikinmu a idon masu zuba jari na kasashen waje,” kamar yadda ya shaida wa Anadolu.
Rasaki Dauda, wanda shi ne shugaban sashen nazarin tattalin arziki na Jami’ar Redeemer da ke garin Ede a yankin kudu maso yammacin Nijeriya, ya yi gargadin cewa yajin aikin zai yi matukar tasiri wajen haƙo man fetur a Nijeriya. Ya ce za a samu raguwar yawan man da ake fitarwa idan aka ci gaba da yajin aikin.
Wani ɗan kasuwa Abdul Bala ya ce ya yi asarar kimanin Naira miliyan huɗu a harkokinsa da yake yi a tashar jiragen ruwa ta Apapa da ke Legas tun ranar Talata da aka fara yajin aikin.
Wannan shi ne karo na biyar da ake yajin aikin a bana a Nijeriya.
Sulhu bai yi nasara ba
Gwamnatin tarayyar Nijeriyar ta yi wata ganawa a ofishin Babban Mai bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro, Nuhu Ribadu da shugabannin ƙungiyar ƙwadagon da kuma Ministan Ƙwadago Simon Lalong, sai dai ba a cimma wata sahihiyar matsaya ba.
Amma a ƙarshen taron Mista Lalong da shugabannin ƙungiyoyin ƙwadagon da suka halarta sun ce an yi tattaunawa mai fa'ida a kan batun yajin aiki.
Sannan ƴan ƙwadagon sun yi wa gwamnati alkawarin komawa su tuntuɓi mambobinsu da kuma rarrashinsu don janye yajin aikin.
Amma a wani bidiyo da gidan talabijin na ƙsa NTA ya wallafa a shafinsa na X, shugabannin TUC da NLC duk sun ce ba a janye yajin aikin ba, "har sai gwamnati ta biya musu buƙatun da suke nema sannan su janye," kamar yadda shugaban TUC ya shaida wa gidan talabijin na Channels a wata hirar daban.
Daga cikin buƙatun nasu har da na neman a kama tare d agurfanar da waɗanda suka ci zarafin shugaban NLC a birnin Owerri na Jihar Imo.
Tun da fari a ranar Laraban Nuhu Ribadu ya nemi afuwar ƙungiyoyin ƙwadagon kan abin da aka yi wa shugaban NLC Joe Ajaero a Imo ɗin ranar 1 ga watan Nuwamba, yana mai cewa tuni an kama waɗanda suka aikata masa hakan har ma an fara bincike.