Nijeriya ta caccaki Amurka kan shawarwarin da ta bayar cewa otel-otel din kasar na fuskantar barazanar tsaro.
Gargadin na Amurka zai iya jawo “fargaba ba gaira ba dalili” tare da yi wa tattalin arziki illa, a cewar Ministan Watsa Labarai Mohammed Idris.
Ofishin Jakadancin Amurka a Nijeriya ya fitar da wani gargadi a ranar Juma’a da ke cewa “manya-manyan otel-otel a manyan biranen ƙasar na fuskantar barazanar tsaro,” amma ya ce hukumomin tsaron ƙasar na aiki tuƙuru don magance waɗannan barazana.
“Waɗannan shawarwari ba sa kawo komai idan ba tayar da fargaba ba, kuma za su iya yin mummunan tasiri a kan tattalin arziki, ba a ma maganar tasirinsu na daƙushe ƙoƙarin gwamnati na jawo hankalin masu zuba jari,” kamar yadda Minista Idris ya shaida wa taron manema labarai a ranar Litinin.
Barazanar tsaro
Ministan ya jaddada cewa gwamnatin tana ci gaba da bai wa tsaron ƴan ƙasa da sauran baƙin da ke shiga cikinta muhimmanci, ta hanyar “ɗaukar ƙwararan matakai.”
A bara, Amurka ta fitar da irin wannan argaɗin tana mai shawartar Amurka da su guji yin tafiye-tafiye zuwa jihohin Nijeriya da dama saboda “barazanar ta’addanci.
Nijeriya ta bayyana rashin jin daɗinta a kan hakan, kuma a hankali Amurka ta janye gargaɗin tsaron.
Ƙwararru sun kuma dasa ayar tambaya a kan irin wadannan shawarwari da Amurka ke bayarwa a kan ƙasashe a faɗin duniya.
Dakarun tsaron Nijeriya suna ƙoƙarin shawo kan matsalolin tsaro da ake fama da su na ƙungiyar Boko Haram da gungun masu satar mutane don kuɗin fansa a ƙasar.