Nijeriya ta karbi kason farko na allurar riga-kafin cutar maleriya R21 har 846,000 daga kamfanin Gavi, the Vaccine Alliance.
Ƙaddamar da alluran riga-kafin na ranar Alhamis ya samu halartar jami'ai daga Ma'aikatar Lafiya da Hukumar Kula da Kiwon Lafiya a Matakin Farko ta Nijeriya (NPHCDA) da kuma sauran abokan hulɗa.
Ministan Lafiya, Muhammad Ali Pate, ya bayyana isowar alluran riga-kafin a matsayin wata muhimmiyar nasara a ƙoƙarin gwamnati na kawar da cutar maleriya daga ƙasar.
Ya ce za a fara rarraba alluran ne a jihohin da suka fi fama da cutar, musamman Kebbi da Bayelsa,, kuma za a yi amfani da su a matsayin maganin warkar da cutar.
Minista Pate ya kuma warware zare da abawa a kan ingancin riga-kafin, yana mai ba da tabbacin cewa yana da matuƙar tasiri ga warkar da cutar maleriya.
Kazalika, Darakta Janar na hukumar NPHCDA, Muyi Aina ya yi bayani kan yadda za a rarraba su, yana mai cewa za a kafa tawagar da za ta tabbatar cewa an tsara yadda komai zai kasance tun daga rarrabawa har zuwa yi wa mutane a kan lokaci.
Aina ya ce ana sa ran za a sake karbar wasu alluran 140,000 a 'yan watanni masu zuwa. Za a dinga yin wannan allura ne sau biyu ga duk mutum daya.