Bagudu ya ce kuɗin na cikin tsarin wanda za a kashe ne a shekarar 2023. Hoto: Atiku Bagudu X

Majalisar zartarwa ta gwamnatin Nijeriya ta amince da wani ƙarin kasafin kuɗi na naira tiriliyan 2.176, (dala biliyan 2.8) don amfani da su a “wasu ayyuka na gaggawa” da suka haɗa da na soji da tsaro, kamar yadda Ministan Harkokin Kasafin Kuɗi Atiku Bagudu ya bayyana a ranar Litinin.

Bagudu ya ce kuɗin na cikin tsarin wanda za a kashe ne a shekarar 2023.

“Wannan ƙarin kasafin kuɗi an yi shi ne don yin wasu ayyuka na gaggawa da suka haɗa da naira biliyan 605 a fannin aikin soji da tsaron ƙasa,” kamar yadda Bagudu ya shaida wa manema labarai bayan wani taron majalisar zartarwa a Abuja.

“An yi hakan ne don a ci gaba da tabbatar da nasarorin da ake samu a fannin tsaro da kuma adana wasu kuɗaɗe da hukumomin tsaron ke buƙata. Kazalika an ware naira biliyan 300 don gyaran gadoji a ƙasar.”

‘Sauye-sauye masu tsauri’

Shugaba Bola Tinubu ya gaji tulin bashin da ake bin ƙasar a lokacin da ya yi rantsuwar kama mulki a watan Mayu, kuma yana cikin matsin lambar warware matsalolin da suka yi wa tattalin arzikin ƙasar dabaibayi, don ya ci gaba da samun goyon bayan al’umma bayan da ya ƙaddamar da wasu sauye-sauyen da masu sharhi suka ce sun ƙara ta’azzara halin matsi da mutane ke ciki.

Ya cire tallafin man fetur da gwamnati ta shafe gomman shekaru tana biya, lamarin da ya jawo tashin gwauron-zabin farashin man a ƙasar, tare da rage darajar naira da fiye da kashi 50%, abin da ya jawo hauhawar farashi a ƙasar, wacce ita ce ta fi fitar arzikin man fetur da kuma yawan jama’a a Afirka.

Bagudu ya ce gwamnati za ta bai wa iyalai miliyan 15 naira 25,000 kowannensu daga watan Oktoba zuwa Disamban 2023, a cikin dala biliyan 800 din da ƙasar ta karɓo rance a watan Afrilu daga Bankin Duniya, don taimaka wa wajen rage raɗaɗin da mutane ke ciki.

Ya ƙara da cewa za a yi amfani da sauran kuɗaɗen na ƙarin kasafin ne don sayen kayan amfanin gona ga manoma da gyaran hanyoyi da gina sabbi a faɗin ƙasar, da kuma biyan ƙarin albashin da aka yi wa ma’aikatan gwamnatin tarayya daga watan Satumba zuwa na Disamba.

Majalisar zartarwar Nijeriya ta kuma amince da wani tsarin kashe naira tiriliyan 26.01 (dala biliyan 34) a kasafin kudin shekarar 2024.

TRT Afrika da abokan hulda