Gwamnatin Nijeriya ta ce ƙasar na fama da matasanancin ƙarancin abinci mai gina jiki, inda take cikin ƙasashen duniya da matasalar ta fi ƙamari.
Minsitan Lafiya na ƙasar Farfsa Muhammad Ali Pate wanda ya bayyana haka a shafinsa na X ranar Alhamis, ya ce matsalar ta fi ƙamari a yankunan arewa maso yamma da arewa maso gabashin ƙasar.
Farfesa Pate wannan ya ce matsalar abar ta da hankali ce, ganin cewa rahoton Asusun Tallafa wa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya UNICEF ya nuna cewa kimanin yara miliyan biyu ne ke fama da matsanancin ƙarancin abinci mai gina jiki, inda 40% na yaran suke a jihohi shida.
“Fiye da yara miliyan shida ne ke fama da matsakaicin ƙarancin abinci mai gina jiki, sannan mata da dama (masu ciki da masu shayarwa) na fama da ƙarancin sinadaran abinci mai gina jiki,” a cewar Farfesa Pate.
Ya ƙara da cewa manyan matsalolin da ke haifar da matsalar suna da dama, da suka hada da “yanayin shugabanci da karuwar jama’a inda mutane da dama ke dogara da wasu saboda tsabar talauci, da wasu sassan arewa ke fama da shi da kuma rashin tsaro a yankin, da yanayin cimaka, da rashin tallafa wa mata ta fannin tattalin arziki,” a cewarsa.
“A yanzu muna fama da gagarumar matsala. Magance matsalar karancin abinci mai gina jiki ba wai kawai abin da ya kamata mu yi ba ne, yana ma da muhimmanci wajen inganta lafiya da tabbatar da ci gaban ƙasa mai ɗorewa.
“A yau an kira taronmu na ministoci da abokan hulda domin tantance kokarin da ake yi na tunkarar wannan matsala yadda ya kamata. Mun yaba da gudunmawar da muka samu daga abokan aikinmu daga cikin gwamnati da suka halarta.
"An ƙarfafe mu da yiwuwar samun dala miliyan 30 ba tare da ɓata lokaci ba daga shirin #ANRIN na Bankin Duniya, da kuma yiwuwar samun wani tallafin daga Asusun Kula da Abinci mai Gina Jiki ga Yara wato Child Nutrition Fund.
“Mun kafa tawagar ayyuka ta ministoci don samar da ingantaccen tsarin aiki cikin sauri, mai mayar da hankali kan tattara albarkatu cikin gaggawa da kuma ayyuka masu amfani don isar da mafita ga waɗanda suka fi buƙatarsu.
Yara da mata
Wannan shirin ya yi la'akari da wahalhalun da yara da mata ke fuskanta,” a cewar Minista Pate. Ya jaddada muhimmanci haɗin kai tare da kawar da son zuciya don a yi aiki yadda ya dace, yana mai cewa za su sa ido kan don tabbatar da an y adalci a ayyukan taimakon da suka haɗa da rabon kayayyakin abinci da magunguna na gina jiki.
Ministan Lafiyar ya ce za su yi amfani da samar da abinci da magunguna da sauran abubuwan da suka shafi al'umma, tare da ƙarfafawa da haɓaka fiye da wuraren jinya 1,192 da aka riga aka fara aiki, galibi a cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko.
A ƙarshe ministan ya yi kira ga gwamnatocin jihohi da su kasance cikin shirin ko-ta-kwana da taimakawa hukumomi da dama a jihohinsu, da kuma samar da ƙarin abubuwan da ake buƙata don tafiyar da wannan mataki mai wahala.
“Akwai kyakkyawan fata, kuma Nijeriya za ta fita daga cikin wannan yanayin ta hanyar jajircewar Shugaba Bola Ahmed Tinubu, a cewar Pate.