Hukumar da ke yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Nijeriya NDLEA, ta ce ta kama tireloli biyu dauke da tabar wiwi a Legas da nauyinsu ya kai kilo 8,852.
A wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Lahadi, ta ce ta yi nasarar kama motocin ne bayan jami’anta sun yi musayar wuta da masu rakiyar motocin wiwin tsawon minti talatin.
Hukumar ta ce tun da farko jami’anta sun yi kokarin tsayar da motocin da ke dauke da tabar amma suka ki tsayawa inda suka kara gudu, daga nan ne aka yi musayar wuta.
“Bayan da jami’an NDLEA suka sha karfinsu, direbobin motocin da kuma ‘yan bindigan da suka rako su sai suka gudu cikin daji inda suka bar motocin da kuma tabar,” in ji sanarwar ta NDLEA.
Hukumar ta bayyana cewa tirelar farko tana da jan fenti inda take dauke da buhu 149 na wiwi da nauyinsu ya kai kilo 6,548, sai kuma ta biyu tana da shudin fenti inda take dauke da buhuna 53 da nauyinsu ya kai kilo 2,304.
Hakan ya sa jumullar buhunan ya kama 202 sai kuma nauyinsu ya kama 8,952.
Hukumar ta kuma ce jami’anta suna ci gaba da neman wanda ya shigo da haramtattun kayayyakin.
Duk da yunkurin da hukumar ke yi na dakile fataucin miyagun kwayoyi, amma ana ci gaba da samun masu safararsu da kuma hada su a cikin kasar.
Ko a makon da ya gabata sai da hukumar ta NDLEA ta ce ta kama miyagun kwayoyi da suka hada da tabar wiwi a Legas.
Haka kuma ta ce ta gano wani kamfani da ake hada A-Kuskura a Jihar Adamawa.