Kwanaki biyu bayan hukumar hana sha da da fataucin miyagun kwayoyi ta Nijeriya, NDLEA ta yi umarnin saka ido kan yaduwa nau'in gas na "lauhing gas", mai kashe laka da saka dariya, hukumar ta sanar da kama tarin sindarin a garuruwa biyu na kasar a ranar Juma'a.
Hukumar ta ce ana samun masu amfani da sinadarin na nitrous oxide, wanda aka fi sani da "laughing gas" domin jin dadi da sa maye.
Shugaban ya umarci duka ofisoshin hukumar a fadin Nijeriya da su fara daukar mataki kan masu sayar da gas din da masu amfani da shi ba bisa ka'ida ba.
Hukumar ta ce kamen da ta yi ya biyo bayen tsegunta wa jami'anta a Apapa, game da shigo da sinadarin a ranar Laraba 12 ga watan nan na Yuli.
Daga nan ne ta damke kwantena biyu masu lambobin MSKU 7626856, da kuma MSKU 7689448.
Daga bisani An cafke wanda ya shigo da kayan sunansa Stephen Eze, dan shekara 30, da dillalinsa, Michael Chukwuma, don karin bincike.
Haka nan kuma, a yayin sintirin jami'an hukumar NDLEA a birnin Owerri zuwa Anacha na Jihar Imo ranar Alhamis, sun damke katan uku mai dauke da gwangwani 18 na sinadarin, mai nauyin kilogiram 11.5. An nufi birnin Fatakwal ne da kayan.
Sinadarin na nitrous oxide, gas ne mara kala, wanda ake amfani da shi don gusar da hankali, da kawar da radadi. Yawanci likitocin hakori ne da sauran ma'aikatan lafiya suke suke amfani da shi.
A yanzu dai, mutane a Nijeriya sun fara amfani da gas din a matsayin sinadarin saka maye, a wuraren liyafa da sheke-aya.
Yawanci ana zuba sinadarin ne a cikin balo, daga nan sai a rika shaka, don a yi maye.