Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Nijeriya (NAFDAC) ta rufe wata haramtacciyar masana’anta da ke samar da jabun kayan kwalliya a rukunin shagunan Benue Plaza da ke Filin Bajekoli a jihar Legas da ke kudancin ƙasar.
NAFDAC ta bayyana hakan ne a wani sako da ta wallafa a shafinta na X a ranar Talata, inda ta ce an rufe masana’antar ne bayan da jami’anta suka kai samame tare da gano wasu sinadarai da kayayyakin da ba su da rajista, da kuma waɗanda lokacin amfani da su ya wuce suka lallace.
A yayin gudanar da aikin, hukumar ta NAFDAC ta kama fiye da kwali 1,200 na kayan kwalliya na jabu.
Kayayyakin sun hada da kananan mazubai na haɗe-haɗe, da sinadarai marasa tambari da ma wasu na'urori, inda aka ƙwace aka kai su ofishin NAFDAC domin ci gaba da bincike.
“Hukumar ta ƙiyasta darajar kayayyakin da aka ƙwace a farashin kan titi inda ya kai kusan naira miliyan 50,” in ji NAFDAC.
Hukumar ta kuma bukaci jama’a da su yi taka-tsan-tsan wajen sayen kayan kwalliya tare da kai rahoton duk wani abin da ake zargi ga ofishin NAFDAC mafi kusa.