NAFDAC ta rufe manyan kasuwannin magunguna uku na Nijeriya

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Nijeriya NAFDAC ta rufe wasu manyan kasuwannin magunguna na ƙasar – a matsayin wani ɓangare na yaƙi da jabun magunguna, marasa inganci, da kuma wadanda aikinsu ya ƙare, a fadin kasar.

Kasuwannin sun haɗa da ta Idumota a Lagos, wadda ita ce babbar kasuwar magunguna ta Afirka, da kasuwar magani ta Anaca da ke Anambra da kuma ta Ariaria da ke Aba.

Hukumomin tsaro da suka hada da Sojoji da ‘Yan Sanda da Hukumar Kula da Lafiyar Jama’a, da Hukumar Kula da Magunguna ta Nijeriya, na hada kai da Hukumar NAFDAC domin tabbatar da an bi wannan doka.

A wata sanarwa da NAFDAC ta wallafa a shafinta na X ranar Alhamis, hukumar ta ce ya zuwa yanzu dai an ƙwace manyan motoci bakwai cike da lodin magunguna da ake zargin na jabu ne da kuma waɗanda wa’adinsu ya ƙare.

NAFDAC ta ce za ta cigaba da jajircewa wajen kare lafiyar al’umma ta hanyar kawar da magunguna marasa inganci da bazuwarsu.

“Masu shagunan suna yin aiki tare da umarnin hukumar, yayin da jami'an tsaro ke tabbatar da gudanar da aiki cikin kwanciyar hankali,” in ji sanarwar.

A cikin bidiyon da NAFDAC ta wallafa a shafin nata na X, an ga yadda shugabar hukumar Mojisola Adeyeye ke jagorantar samamen, wanda aka fara shi tun ranar Lahadi.

Hukumar ta ce ta fara hakan ne saboda damuwar da ke ƙaruwa kan yaduwar jabun magunguna masu yi wa rayuwar al’umma barazana.

Farfesa Mojisola ta ce maƙasudin wannan aiki shi ne don a tabbatar da cewa idan mutane suka sha magani to ya yi musu aiki.

“Babban dalilin wannan aiki shi ne don a kare ku da ni kaina. Don a tabbatar idan mun sha magani ya yi mana aiki.

“Don mu tabbatar idan aka ba wa yara magani bai kashe su ba, saboda maganin ba shi da illa.”

Shugabar ta NAFDAC ta ƙara da cewa aikin na yaki da jabun magunguna ya haɗa da “kula da sha’anin sayar da magunguna. Wa ke sayarwa, wa yake samar da shi, an amince da su ko a’a.”

“Akwai shaguna fiye da 5,000 a kasuwannin magunguna barkatai, bai kamata su kasance a bude barkatai ba. Kamata ya yi a ce suna aiki bisa tsari a matsayin cibiya.

“Za mu yi aikin kawar da su a Legas da Aba da Anaca, amma kafin sannan dole mu karɓi ragamar harkar saboda mun damu da mutanenmu,” in ji ta.

TRT Afrika