Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Legas LASEMA ta bayyana cewa an yi asarar kayayyaki na miliyoyin naira sakamakon gobarar da ta tashi a kasuwar sayar da kayayyakin motoci ta Idumota da ke Legas.
A wata sanarwa da babban sakataren LASEMA wato Olufemi Oke-Osanyintolu ya fitar, ya bayyana cewa gobarar ta tashi ne a kasuwar a ranar Juma’a da dare.
Oke-Osanyintolu ya bayyana cewa binciken wucin-gadi da aka gudanar ya gano cewa akwai shaguna da dama waɗanda ke sayar da kayayyakin motoci waɗanda suka ƙone.
“Bayan samun kiran gaggawa ta layukanmu na 767/112, da misalin 10:30 na dare, Hukumar Bayara da Agajin Gaggawa ta Legas LASEMA ta aika da jami’anta na bayar da agaji daga Lekki da Cappa da Alausa da Ikeja,” in ji shi.
“A lokacin da jami’an LASEMA suka isa da misalin 10:55 na dare, an gano cewa shagunan da ake amfani da su domin sayar da kayayyakin motoci gobara ta laƙume su," kamar yadda ya ƙara da cewa
Oke-Osanyintolu ya kuma bayyana cewa babu wanda ya mutu ko kuma ya jikkata sakamakon wannan gobara.
Haka kuma babu tabbacin ainahin abin da ya haddasa gobarar.