Limaman Masallatan Juma’a na Jihar Neja da Kwamitin Malamai da iyayen yara 100 da gwamnati ke son aurar da su, sun ce sun ɗauki matakan da suka ga sun dace na tabbatar da yiwuwar aurarrakin, wanda Ministar Mata ta Nijeriya ke ƙalubalanta.
A wata sanarwa da daraktan da ke kula da harkokin addini na jihar ya fitar a yau Juma’a, ta ce masu ruwa da tsakin sun yi taron ne a Minna, inda suka tattauna kan batun umarnin kotu da kuma ƙarar Shugaban Majalisar Dokokin jihar Barista Abdulmalik Sarkin Daji da Ministar Matan ta shigar, kan batun ɗaukar nauyin auren marayu 100 da aka shirya yi a ƙaramar hukumar Mariga.
Batun aurar da ‘yan matan ya jawo ce-ce-ku-ce sosai a Nijeriya, wanda Minsitar Matan Uju Kennedy-Ohanenye ta shigar da ƙara kotu don neman a dakatar da yin sa a ranar 24 ga watan Mayu kamar yadda aka tsara tun da farko.
A ganin Ministar, ‘yan matan wadanda yawanci marayu ne da suka rasa mahaifansu a hare-haren ‘yan bindiga da ya addabi jihar, “wani abu daban suka cancanci a yi musu.” kuma ma’aikatarta na bincike don gano ko su wane ne ‘yan matan 100 da shekarunsu da kuma ko bisa amincewarsy za a yi auren.
Sai dai ko a ranar Juma'a, Minista Uju ta wallafa a shafinta na X cewa ta cimma matsaya tare da Sarkin Kotangora, HRH Alh Mohammed Barau Muazu da Kakakin Majalisar Abdumalik Sarkindaji, kan neman hanyar hadin gwiwa don bai wa ‘yan matan sabuwar rayuwa, amma har yanzu hukuncin Kotun yana nan ba kawar da shi ba.
“Ban janye shari’ata ba har sai mun gudanar da aikin tantance ‘yan matan, sannan za mu sa ‘yan matan su shiga makarantu, da koyar da sana’o’in hannu da kuma karfafa wa ‘ya’ya mata, babban burin ma’aikatarmu shi ne tabbatar da ganin an samar da walwala kuma an tabbatar da bukatun ‘yan matan”.
Sanarwar daraktan harkokin addinan ta ce matakai biyar Limamai da Malamai da Iyayen yaran suka ɗauka kan wannan lamari kamar haka;
1. Za a ɗaura auren marayu 100 a ranar 24 ga Mayu, 2024 kamar yadda aka tsara. Dalili shi ne, babu ta inda auren da aka shirya yi ya saɓa wa kundin tsarin mulkin ƙasa da kuma dokokin addininMusulunci.
2. Mahalarta taron sun buƙaci Ministar Harkokin Mata Mrs. Uju ta nemi afuwar jama'a nan da kwana bakwai ko kuma a dauki matakin shari'a a kanta.
3. Taron ya yi kira ga Shugaban Nijeriya da ya kori Ministar cikin gaggawa domin kauce wa rikicin addini a kasar.
4. Taron ya kuma yi kira ga ɗaiɗaikun jama’a da ‘yan siyasa da su yi koyi da shugaban Majalisar Dokokin kan irin wannan halayya.
5. A karshe taron ya yi kira ga al’ummar Musulman jihar da su ci gaba da kasancewa masu bin doka da oda domin malamai da shugabannin addinin Musulunci na kan gaba a lamarin.