Majalisar Dattawan Nijeriya ta fara sauraron ra'ayoyin jama'a a kan ƙudurin sake fasalin dokar haraji na tsawon kwana biyu, wanda yake samun halartar fitattu daga ɓangaren tattalin arzikin ƙasar.
Sanata Sani Musa, Shugaban Kwamitin Kuɗi na Majalisar Dattijan, ya tabbatar da cewa zaman zai zama na ƙeƙe-da-ƙeƙe kuma bisa abin da zai amfani ƙasar.
An shirya zaman sauraron ra'ayoyin ne da zummar zamannatar da dokokin harajin Nijeriya don ya yi daidai da zahirin yanayin tattalin arzikin da ake ciki, yayin da za a tabbatar da adalci da saka kowane ɓangare a tafiyar da ma inganta tsarin harajin.
Sanata Musa ya nemi masu ruwa da tsaki da ma al'umma da su taka rawa sosai, yana mai jaddada cewa haɗa hannu yana da muhimmanci wajen inganta tsare-tsaren da za su ƙarfafa tattalin arziki da cigaban ƙasa.
Gidan rediyon Tarayyar Nijeriya FRCN ya rawaito cewa daga cikin mahalarta taron akwai Ministan Kudi Wale Edun, da shugaban hukumar tattara haraji ta tarayya FIRS Zacch Adedeji, da shugaban kamfanin man fetur na Nijeriya NNPCL Mele Kyari, da mambobin Majalisar Zartarwa ta Tarayya da shugaban hukumar kwastam Adewale Adeniyi.
Shugaba Bola Tinubu ya nemi Majalisar Dattijai da ta samar masa da dokokin da za su yi aiki daga ƙudurin, wata huɗu bayan da aka aika wa majalisar ƙudurorin sauya fasalin harajin don su amince da su.
Masu ruwa da tsaki daban-daban sun nuna goyon bayansu ga kudurorin da ake ta cece-kuce a kai a baya a yayin wani taron jin ra'ayin jama'a da kwamitin majalisar dattijai kan harkokin kudi ya yi a Abuja ranar Litinin.