Cutar kwalara na sanadin mutuwar dubban yara a fadin duniya. Hoto/Reuters

Fiye da mutum 350 ne suka mutu sakamakon kwalara a watanni tara na shekarar nan, ƙari da kashi 239 idan aka kwatanta da alƙaluman shekarar da ta gabata a daidai wannan lokaci, in ji Cibiyar Yaƙi da Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Nijeriya (NCDC).

Cutar kwalara da ake ɗauka daga ruwan sha mara tsafta, ta zama ruwan dare a Nijeriya inda hukumomin lafiya ke cewa babu tsaftataccen ruwan a yankunan karkara da unguwannin marasa galihu da ke birane.

NCDC ta ce mutane 359 ne suka mutu daga watan Janairu zuwa Satumban bana, inda a irin wannan lokaci na shekarar da ta gabata aka samu rasa rayuka 106.

Adadin waɗanda suka kamu da cutar ta kwalara ya ƙaru zuwa 10,837, daga 3,387 a bara, inda mafi yawan waɗanda suka kamu yara ne 'yan ƙasa da shekaru biyar.

Lagos, babban birnin kasuwanci na Nijeriya ne ke da adadi mafi yawa na mutanen da suka kamu da cutar, in ji NCDC.

Mahukunta a Borno da ke arewa maso-gabashin Nijeriya a ranar Juma'a sun bayyana ɓarkewar cutar a jihar, wadda ta yi fama da ambaliyar ruwan da ta raba mutane miliyan biyu da matsugunansu.

Reuters