NUC yajin aiki

Kungiyoyin Ƙwadagon Najeriya NLC da TUC sun dakatar da yajin aikin da aka fara jiya a kasar sakamakon neman gwamnati ta ƙara mafi karancin albashi da kuma adawa da ƙarin kudin wutar lantarki.

A yau Talata ne shugaban kungiyar kwadago ta TUC Festus Osifo ya sanar da janye yajin aikin a Abuja yayin wani taro da shugabannin kungiyoyin kwadagon.

Tun da fari a ranar Litinin da yamma ƙungiyoyin ƙwadagon da wakilan gwamnatin tarayyar Nijeriya sun yi wata ganawa inda aka cimma matsaya hudu, ciki har da aniyar Shugaba Tinubu ta ƙara N60,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi a ƙasa.

Gidan talabijin na Channels ya rawaito Mista Osifo yana cewa "Bayan wani taron haɗin gwiwa na ƙungiyoyin ƙwadago na TUC/NLC sun amince da sassauta yajin aikin ne na tsawon mako guda ba tare da ɓata lokaci ba,

Shugaban ƙungiyar ƙwadagon ya ce nan ba da jimawa ba za a fitar da bayanai a kan abubuwan da aka cim ma a wajen taron.

TRT Afrika