Shugaba Tinubu ya yi maraba da hukuncin. Hoto: Tinubu Facebook

Kotun sauraren kararrakin zaben Nijeriya ta tabbatar da Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban kasar a zaben da aka yi na watan Fabrairun 2023.

Kotun, wacce ta gabatar da hukuncin a Abuja ranar Laraba, ta yi watsi da korafe-korafen da 'yan takarar shugabancin kasar a zaben 2023, Atiku Abubakar na Jam’iyyar PDP da Peter Obi na Jam’iyyar LP suka shigar na neman soke zaben Shugaba Tinubu.

Alkali Haruna Tsammani ne ya yanke hukuncin bisa taimakon alkalai hudu - Mai Shari'a Stephen Adah, Mai Shari'a Monsurat Bolaji-Yusuf, Mai Shari'a Moses Ugo da kuma Mai Shari'a Abba Mohammed.

Sai dai Jam’iyyar Labour ta yi watsi da hukuncin kotun. Sakataren Watsa Labarai na LP Obiora Ifoh ya ce ba a yi adalci ba a shari’ar kuma ba a bi muradun al’umma ba.

“’Yan Nijeriya shaidu ne kan yadda aka yi fashin zabe ranar 25 ga watan Fabraiun 2023, wanda aka yi Allah wadai da shi a fadin duniya amma Kotun Sauraron Karar Zaben ta yi biris da wannan abu,” ya ce.

Ita ma Jam'iyyar PDP a tata sanarwar ta ceba ta yarda da hukuncin ba "don cike yake da kura-kurai. PDP da lauyoyinta za su dauki mataki na gaba," in ji sanarwar jam'iyyar.

Shi kuwa Shugaba Tinubu ya yi maraba da hukuncin ne a wata sanarwa da ya fitar jim kadan bayan hukuncin kotun, inda ya ce hukuncin ya kara masa azamar daukar nauyin da ya rataya a wuyansa na yi wa 'yan Nijeriya aiki ba tare da nuna bambanci ba.

Watsi da korafe-korafen da Jam’iyyar Labour ta shigar

An yi watsi da karar da Jam’iyyar LP da dan takararta Peter Obi suka shigar kan zargin cewa an tafka kura-kurai a yayin kada kuri’a, inda kotun ta ce sun gaza yin bayanin yadda suka ce sun yi nasarar samun mafiya yawan halastattun kuri’un da aka kada a zaben shugaban kasa na watan Fabrairun.

A yayin da yake karanto korafe-korafen da ake shari’a a kansu, Mai Shari’a Abba Bello Mohammed ya ce jam’iyyar LP ta yi zargin cewa an tafka kura-kurai da tursasa wa masu zabe da ba da cin hanci don kwace musu kuri’u, musamman a jihohin Ribas da Binuwai da Legas da Taraba da Imo da Osun amma ta kasa kawo sunayen rumfunan zaben da aka yi hakan.

Mai Shari’a Mohammed ya karkare da cewa Jam’iyyar LP ta gaza tabbatar da dukkan zarge-zargen da ta yi a aringizon kuri’u da APC ta yi da rage yawan kuri'un ita LP din.

Kotun sauraron kararrakin zaben ta kuma yi watsi da bayanan da shaidu 10 cikin 13 da Peter Obi da LP suka gabatar. Babban alkalin shari;ar, Mai Shari'a Haruna Tsammani ya ce bayanan shaidun na rantsuwar da suka yi ba su cancanta ba.

Kotun ta sake yin watsi da bukatar Jam’iyyar Labour da Peter Obi da ke neman a soke zaben Tinubu kan batun kwace dala miliyan 460 a wata Kotun Amurka.

Ta yi watsi da ikirarin Peter Obi da jam’iyyarsa cewa sun samu kashi 25 cikin 100 na jumullar kuri’un Babban Birnin Tarayyar Abuja.

An kori korafin APC kan LP

Kotun ta yanke hukuncin cewa ita ma Jam’iyyar APC ba ta iya gabatar da wata kwakkwarar hujja kan kalubalantar Peter Obi na Labour da take yi ba, na cewa bai cancanta ya tsaya takara a Jam’iyyar Labour ba.

Jam’iyyar APC da dan takararta Tinubu a cikin korafinsu sun ce babu sunan Peter Obi a jerin sunayen mambobin Jam’iyyar Labour da aka aike wa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar a ranar 25 ga watan Afrilun 2022, kuma hakan ya take dokar sashe na 77 na Dokar Zabe ta 2022.

Mai Shari’a Mohammed a lokacin da yake mika wa jagoran shri’ar Alkali Tsammani, ya ce wannan batun magan ce ta cikin gida ga Jam’iyyar Labour.

Sannan kuma Mai Shari’a Mohammed ya yi watsi da korafin APC cewa bai kamata dan takarar PDP Atiku Abubakar da na LP Peter Obi su yi hadaka wajen kalubalantar sakamakon zaben ba.

Korafe-korafen Atiku Abubakar

Kotun Sauraron Kararrakin Zaben ta yi watsi da korafin Atiku Abubakar da ya nemi a soke sakamakon zaben shugaban kasa na jihohin Kano da Legas.

Kotun ta ce masu korafin ba su hada da Peter Obi da Rabiu Kwankwanso ba wadanda suka samu kuri'u mafi yawa a jihohin biyu.

Kotun ta kuma yi watsi da korafin Atiku Abubakar da na jam’iyyarsa ta PDP kan zargin cewa Shugaba Tinubu yana da takardar shaidar zama dan kasashe biyu da kuma na zargin tuhumarsa da safarar kwaya.

Sai kuma Mai Shari’a Moses Ugo shi ma ya yi watsi da karar da ya karanto kan batun rashin cancantar Tinubu saboda rashin shaidar karatu, inda ya ce wannan sabuwar kara ce, kuma ba zai yiwu Atiku da PDP su shigar da sabon korafin da tun farko ba su gabatar da shi ba.

Korafin Jam’iyyar APM

Kotun ta ayyana cewa ba ta da hurumin sauraron korafin Jam’iyyar APM da ke kalubalantar rashin takardun shaidar karatun Tinubu da Kashim Shettima.

Da yake karanto shari’un, Mai Shari’a Haruna Tsammani ya ce dukkan korafe-korafen da aka gabatar wa Kotun Sauraron Kararrin Zaben duk abubuwa ne da suka shafi wadanda suka faru bayan zabe da suka kamata a gabatar da su a Babbar Kotu.

Alkalan da suka saurari karar

Alkalai biyar ne suka saurari karar karkashin jagorancin Mai Shari’a Haruna Tsammani.

Sai sauran alkalai hudu da suka taimaka masa da suka hada da Mai Shari'a Stephen Adah da Mai Shari'a Monsurat Bolaji-Yusuf da Mai Shari'a Moses Ugo da kuma Mai Shari'a Abba Mohammed.

Manyan mutanen da suka halarci kotun

Manyan 'yan siyasa da jami'an jam'iyyun kasar ne suka hallara a kotun domin ganin yadda hukuncin zai kaya.

Wadanda ke halartar zaman kotu sun hada da mataimakin shugaban Nijeriya Kashim Shettima da shugaban jam'iyyar APC Abdullahi Umar Ganduje da wasu gwamnonin jihohi na jam'iyyar.

Kazakila gwamnan jihar Bauchi Bala Mohamed na jam'iyyar PDP na cikin wadanda suka je kotun.

An watsa shari'ar kai-tsaye ta gidajen talabijin da sauran kafofin watsa labarai.

Hukumomin tsaron Nijeriya sun karfafa tsaro a fadin kasar saboda fargabar barkewar tarzoma, suna masu shan alwashin dakile duk wani yunkuri na tayar da zaune tsaye.

TRT Afrika