Wata Babbar Kotu a Abuja da ke Nijeriya ta dakatar da Babban Bankin Nijeriya CBN daga sakar wa gwamnatin jihar Ribas kason kudinta na wata-wata.
A hukuncin da ta yanke a ranar Laraba, Mai Shari'a Joyce Abdulmalik ta ce dukkan kuɗaɗen wata-wata da aka tura wa Gwamnan Jihar Ribas Siminalayi Fubara tun daga watan Janairun wannan shekarar take dokar kundin tsarin mulki ne, kuma dole a dakatar da hakan.
Alkaliyar kotun ta ce gabatar da kasafin kudin shekarar 2024 da Fubara ya yi a gaban ‘yan majalisar dokokin Ribas mai wakilai hudu take dokar kundin tsarin mulkin kasar ne.
Mai Shari’a Abdulmalik ta ce abin da gwamnan ya yi babban cin mutunci ne ga kundin tsarin mulkin 1999.
Daga nan ne alkaliyar ta hana CBN da Akanta Janar na Tarayya da Bankin Zenith da Bankin Access Bank ci gaba da bai wa Fubara damar samun kuɗaɗe daga asusun tattara kudaden shiga da tarayya.
Turka-turka
Tun da farko a watan Oktoba ne Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja ta tabbatar da hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yanke na ware naira biliyan 800 da wasu ‘yan majalisar dokokin jihar Ribas su biyar suka zartar wanda Edison Ehie ke jagoranta.
Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yi watsi da ƙarar da Fubara ya shigar a kan rashin dacewar hakan.
Kotun ta ce Fubara ya janye karar da ya shigar a karamar kotu a kan lamarin don haka ba zai iya fara daukaka kara ba a kan lamarin da bai kalubalanta ba a matakin shari’a.
A hukuncin da aka yanke, kotun ta ce ana sa ran Gwamna Fubara ya yi amfani da tsarin doka ba tsarin amfani da ƙarfi ba, kamar yadda kafar watsa labarai ta Channels ta rawaito.
Sauran hukunce-hukuncen
Kotun ta ci gaba da cewa halin da ake ciki a Majalisar Dokokin Jihar Ribas tamkar mulkin kama-karya ne na Gwamna da kuma abin dariya da ya wuce gona da iri.
Mai Shari’a Omotosho ta soke kasafin kudin Ribas na 2024 da ‘yan majalisa masu goyon bayan Fubara suka amince da shi tare da ajiye batun gabatarwa da kuma zartar da kasafin kudin jihar Ribas na 2024.
A hukuncin da aka yanke Omotoso ta umarci gwamnan da ya sake gabatar da kasafin kudin ga majalisar dokokin da aka kafa bisa doka karkashin Martin Amaewhule.
Sannan ta umarci Fubara da ya saki duk wasu kudaden da aka tara a majalisar dokokin Ribas tare da hana gwamnan yin katsalandan a harkokin majalisar.