An ranstsar da  Bola Tinubu a matsayin sabon shugaban Nijeriya a ranar 29 ga watan Mayu na 2023 / Hoto: AFP

Daga Shamiyya Hamza Ibrahim

A kusan kowace kasa a duniya musamman mai bin tsarin dimokuradiyya irin Nijeriya, matar shugaban kasa na da tasiri sosai a gwamnatin mijinta da ma idon al'umma.

Shi ya sa ma a Nijeriya, kusan duk dan kasar da zai iya jero maka sunayen shugabannin kasar na baya, to tabbas zai iya ambato maka sunayen matayensu.

Kamar yadda kowane shugaba da ya hau mulki kan gabatar da kudurorinsa da tsare-tsaren yadda zai tafiyar da al'amuran mulkin kasa, haka ita ma matar shugaban kasa takan bullo da nata tsare-tsaren.

Duk da cewa dai a kundin tsarin kasa ba a ware ofishin matar shugaban kasa ba, amma a al'adance ana tafiyar da shi.

A hirar da TRT Afirka ta yi da Muhammad Sani Zoro, mataimaki na musamman kan harkokin jama'a da tsare-tsare a ofishin uwargidan tsohon shugaban Nijeriya Aisha Buhari, ya ce matar shugaban kasa tana da karfin iko na fili da na boye kan tafiyar da gwamnatin mai gidanta.

A cewarsa an mayar da wannan matsayi tamkar wata al’ada saboda ganin irin rawar da mata ke takawa a zamantakewar iyali.

''Duk duniya babu inda aka ware wa matan shugabannin kasashe da gwamnoni wani matsayi na musamman ko mataki da za su iya zartar da wani hukunci a kundin tsarin mulki na kasashensu.

"To amma saboda kusancinsu da wadanda suke tafiyar da mulkin, za su iya taka rawa wajen bai wa mazajen nasu shawarar da za ta iya tasiri ga a'umma'' in ji Malam Sani Zoro.

TRT Afrika ta yi nazari kan hanyoyi shida da matan shugabannin kasashe, musamman na Nijeriya za su bi wajen ba da gudumawarsu ga nasarar mulkin mazajensu.

Shugaban Nijeriiya Bola Ahmed Tinubu da matarsa Oluremi Tinubu. Hoto: Shafin Twitter na Tinubu

Shigar da mata cikin harkar mulki

Uwargidan sabon shugaban Nijeriya, Oluremi Bola Tinubu, ita ce ta baya-bayan nan a jerin matan shugabannin kasar da suka zama "First Lady".

Kuma nasarar Remi da mijinta, ta zo a daidai lokacin da Nijeriya ke fafutukar ganin an samu daidaiton jinsi a matakai da dama da kuma kiraye-kirayen kafa doka da za ta karfafa wa mata gwiwa, wato samar da kashi 35 cikin 100 na mukaman da suka kamata mata su samu a kasar.

Hajiya Rabi Galadima, tsohuwar Darakta a Ma’aikatar Harkokin Mata a Nijeriya, ta shaida wa TRT Afrika cewa a yanzu da kasar ta samu sabon shugaba, ya kamata matarsa a matsayinta na gogaggiya a harkar siyasa, ta yi kokarin ganin an bibiyi wannan batu.

‘’Ina fatan matar shugaban kasa Sanata Remi Tinubu za ta bude ido ta yi amfani da kwarewa da matsayinta na tsohuwar 'yar majalisar dokokin kasa, kuma yanzu a matsayin matar shugaban kasa wajen tabbatar da an bai wa mata damarmakin da suka dace," in ji ta.

“Kamar sauran magabatanta, muna sa ran Remi Tinubu za ta dora daga inda aka tsaya a ofishin, ko kuma ta doke tarihin da aka shimfida wajen kara kaimi a shirye-shiryen inganta rayuwar yara da mata a kasar,’’ a cewar Hajiya Saudatu Shehu Mahdi, babbar sakatariyar kungiyar kare hakkin mata ta WRAPA a Nijeriya.

Inganta Lafiyar mata da kanana yara

Daya daga cikin muhimman abubuwan da ke gaban sabuwar gwamnatin Nijeriya shi ne inganta fannin lafiya musamman ta mata da yara, a daidai lokacin da duniya ke kara mayar da hankali wajen rage mace-macen yara da mata a wajen haihuwa.

‘’Duk da cewa gwamnatin da ta shude ta yi irin nata kokarin amma a halin da ake ciki a Nijeriya, idan har ofishin matar shugaban kasa zai mai da hankali wajen samar da shirye- shirye da za su inganta fannin lafiya, ba karamin ci gaba za a samu ba wajen rage yawan mutuwar yara da mata masu juna biyu" a cewar Hajiya Saudatu.

Matar tsohon shugaban Nijeriya Aisha Buhari ta kafa kungiyar Future Assured don tallafa wa mata da yara /Hoto: AA

Dabarun kawar da talauci

Yawancin matan tsofaffin shugabannin kasa a Nijeriya kan hada wani shiri na musamman da zai ba da tallafi domin rage talauci a tsakanin al’umma ta hanyar koya musu sana’o’i tare da ba su tallafi don dogaro da kai.

Matan tsofaffin shugabannin kasa irin su Maryam Babangida da Maryam Abacha da Turai 'Yar Aduwa da Aisha Buhari duk sun yi kungiyoyi na taimakon mata da yara don dakile talauci.

Malam Sani Zorro na ganin irin wadannan tsare-tsare abubuwa ne masu kyau da suka kamata matan shugaban kasa su yi koyi da dabbaka su.

Matan shugabannin kasa da dama da suka wuce sun bijiro da shirye-shiryen tallafa wa mata da yara /Hoto: AA

Hajiya Rabi ta kara da cewa ‘’A wani rahoton da Bankin Duniya ya fitar a farkon shekarar 2023, ya yi nuni da cewa Nijeriya na daga cikin kasashen da ke fama da matsanancin talauci da yunwa."

Yaki da ayyukan cin zarafi ga yara da mata

Wasu daga cikin matsalolin da mata da yara ke fuskanta a kasar ita ce garkuwa da su, sannan akwai batun yi musu fyade.

An sha zuwa makarantun sakandare musamman na 'yan mata ana kwashe su a yi garkuwa da su a Nijeriya.

Wanda ya fi shahara a duniya shi ne na shekarar 2014 da mayakan Boko Haram suka sace 'yan mata 276 na makarantar sakandaren Chibok a jihar Borno.

Maryam Abacha ma ta taimaka wa gwamnatin mijinta ta hanyar bullo da tsari na taimakon talakawa /Hoto: Gumsu Abacha

Sannan ana yawan samun rahotonnin fyade ga yara mata kanana, "akwai bukatar kara yunkuri musamman daga bangaren ofishin uwargidan shugaban kasa, wajen wayar da kan mata.

Wayar da kan zai hada da hanyoyin da za su iya bi don kare kansu daga fadawa inda za a ci zarafinsu da kuma tabbatar da an aiwatar da hukunci kan masu cin zarafin nasu," in ji Hajiya Saudatu Mahdi.

Ba da muhimmanci ga hanyoyin samun ilimi a kasa

Alkaluman rahoton da UNICEF ta fitar a shekarar 2022, sun nuna cewa ‘yan mata miliyan shida ne ba sa zuwa makaranta a Nijeriya.

‘’Ko wacce kasa na muradin samun ci-gaba kuma wannan ci-gaban sai da ilimi ake samunsa, ‘yan Nijeriya na kyautata zaton matar shugaban kasa da kanta za ta ba da gagarumar gudunmawa wajen ganin an samu ilimi a kasar.

"Domin ita ma ta yi karatu mai zurfi kuma ta san amfanin ilimi ga ci gaban kasa, kuma na tabbata za ta so tarihi ya tuna da ita a wannan fannin," in ji Hajiya Rabi.

Stella Obasanjo ma ta aiwatar da irin na ta tsare-tsaren kafin rasuwarta /Hoto: OTHERS

Sakatariyar kungiyar WRAPA ta bayyana cewa "Zai yi kyau idan ofishin matar shugaban kasa zai bullo da wani shiri na musamman da zai duba tsarin ilimin dalibai har da malamai.

"Shirin zai tabbatar da kwarewarsu, tun daga karkara har zuwa jihohi, a shiga lungu da sako wajen tabbatar da cewa kowa ya samu ilimi daidai gwargwado."

Inganta huldar difilomasiyya tsakanin kasa da kasa

Akwai dangantaka mai karfi tsakanin matan shugabannin kasashe da sauran kasashen Afirka da ke rajin tabbatar da samun zaman lafiya a nahiyar, kuma tuni Nijeriya ke ba da gudumawarta wajen cimma wannan muradi.

"Ko a shekarar 2022 sai da kungiyar ta kaddamar da ginin sakatariyarta a babban birnin kasar, Abuja, kuma an zabi matar tsohon shugaban Nijeriya Aisha Buhari a matsayin shugabar kungiyar.

Kazalika akwai wasu ayyuka da matan shugabannin kasashe kan hada kai su yi tare don samun sauki wajen tafiyar da mulkin kasa.

Don haka a nan ma akwai dama sosai ga Remi Tinubu ta dabbaka wannan dangantaka tsakaninta da matan shugabannin kasashen duniya don Nijeriya ta ci moriyar abin, a cewar dukkan masu sharhin.

TRT Afrika