Ministan Ma’aikatar Muhalli Isiaq Salako ya ce  “wannan mataki sako ne babba da ke nuna cewa ba za mu lamunci safarar dabbobin dawa ba.”/Hoto:  Isiaq Salako/Facebook

Gwamnatin Nijeriya ta lalata hauren giwa tan 2.5 na kimanin naira biliyan 10 da ta kwace a yakin da take yi da sarafar dabbobin dawa.

Karamin Ministan Ma’aikatar Muhalli Isiaq Salako ne ya bayyana haka a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Talata da maraice.

"Muna alfaharin kasancewa a kan gaba wurin yaki da safara da kasuwancin hauren giwaye. A yau, mun lalata hauren giwa na kusan naira biliyan goma, wanda shi ne karo na farko a tarihinmu da muka dauki irin wannan mataki a kokarinmu na kare dabbobin dawa," in ji Isiaq Salako.

Salako ya ce za a yi amfani da garin da aka samu bayan nika hauren giwayen wajen gina wani mutum-mutumi a Abuja, babban birnin Nijeriya.

Ya yi kira ga kasashe duniya su hada gwiwa da kasarsa domin yaki da safarar hauren giwaye, yana mai cewa “wannan mataki sako ne babba da ke nuna cewa ba za mu lamunci safarar dabbobin dawa ba.”

Isiaq Salako ya ce za a yi amfani da garin da aka samu bayan nika hauren giwayen wajen gina wani mutum-mutumi a Abuja, babban birnin Nijeriya./Hoto: Isiaq Salako/Facebook

Nijeriya ta dade tana yaki da masu safarar dabbobin dawa. An dakatar da kasar daga yarjejeniyar kare dabbobin dawa ta CITES a 1989 sakamakon karuwar da ta samu ta masu wannan safara.

Sai dai a 2011 an janye dakatarwar sakamakon ci-gaban da ta samu a yaki da safarar dabbobin.

TRT Afrika