Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya amince da biyan sabbin kudaden inshorar rayuwa ga ma’aikatan gwamnatin tarayyar kasar da jami'an leken asiri./ Hoto: Fadar Shugaban Nijeriya

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya amince da biyan sabbin kudaden inshorar rayuwa ga ma’aikatan gwamnatin tarayyar kasar da jami'an leken asiri.

“Wannan ya biyo bayan wata takarda ta neman bukatar hakan ne wacce shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya Folasade Yemi-Esan ta aika wa majalisar zartarwa,” in ji Ministan Watsa Labarai Mohammed Idris, bayan kammala taron majalisar ministoci da shugaban kasa na mako-mako a ranar Laraba.

Ya ce shugaban ƙasa ya amince da kimanin Naira biliyan 9.25 ga kamfanonin inshora na cikin gida 12 don biyan ma’aikatan tarayya idan wani abu ya faru da ya jawo rasa rai a yayin ayyukansu, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Nijeriya ya rawaito.

“Akwai kusan kamfanonin inshora 12 da aka sanya a ciki. Abu ne da aka saba duk shekara inda kamfanonin inshora ke bai wa ma'aikata. Don haka, idan mutum ya mutu ko ya ji mummunan rauni, za su iya neman kudin su yi amfani da su don kada danginsu su sha wahala,’’ in ji shi.

Minista Idris ya ce amincewar wani bangare ne na ƙudirin gwamnatin na bai wa dukkan ma’aikatanta tukuicin da ake bukata wanda zai inganta tsarin aiki da kuma yi wa ‘yan Nijeriya hidima.

Masu sharhi na ganin wannan abu zai taimaka ƙwarai wajen ƙara wa ma’aikata ƙwarin gwiwa da azama, tare da jin cewa gwamnati ba za ta manta da su ba a lokutan da su ko iyalansu ke cikin tsananin buƙatar taimako.

Kazalika a wajen taron majalisar zartarwar na mako-mako, an taɓo batun bai wa ɗalibai bashi wanda gwamnati ta amince da shi tun a bara.

Karamin Ministan Ilimi Yusuf Sununu ya ce gwamnati tana nan a kan matsayarta ta fara bai wa ɗaliban bashi a watan Janairun nan, inda tuni har wani shafin intanet da za a iya neman kudin ya fara aiki.

Ya ce gwamnati ta sanya wannan tsari a cikin kasafin kudinta na shekarar 2024.

Sannan kuma taron majalisar zartarwar ya amince Ministan Tsaro da takwaransa na ma'aikatar ma'adanai su yi duba kan wuraren da ake haƙar ma'adanai ba bisa ƙai'da ba tare da dakatar da hakan.

Sai kuma aka bai wa Ma'aikatar Lafiya izinin ɗaukar ma'aikatan lafiya da ake buƙatarsu da gaggawa don rage cunkoson aiki.

TRT Afrika da abokan hulda