Gwamnatin Jihar Jigawa ta ce bincike zai gudana a bayyane don kare martabar shugabancin jihar./Hoto: Gwamnatin Jigawa

Gwamnan jihar Jigawa a Nijeriya, Malam Umar A. Namadi ya amince da dakatar da Kwamishinan Ayyuka na Musamman, Auwalu Danladi Sankara daga muƙaminsa nan-take, tare da kafa kwamitin da zai bincike shi.

Dakatar wa za ta yi aiki har sai an kammala binciken kwamishinan kan zarge-zargen da hukumar Hisbah ta jihar Kano ta yi kansa, na kama shi da matar aure a wani kango.

Sakataren gwamnatin jihar Malam Bala Ibrahim ya fitar da sanarwar dakatarwar, bayan zargin da aka yi wa kwamishinan. Kuma gwamnatin ta ce bincike zai gudana a bayyane don kare martabar shugabancin jihar.

“Dakatarwar mataki ne na kauce wa matsala don bayar da damar binciken adalci. Mun ɗauki batun da muhimmanci kuma za mu mutunta amanar da al'ummar Jigawa suka ba mu,” cewar sakataren gwamnatin.

Kwamitin bincike

Gwamnatin Jigawa ta kafa kwamitin mutane biyar don ya yi aikin binciken gaskiyar zargin da Hisbah take yi wa kwamishinan, ƙarƙashin sakataren gwamnatin jihar, Bala Ibrahim.

Sauran mambobin kwamitin su ne kwamishinan yaɗa labarai, Sagir Musa Ahmed, da kwamishinan ilimin matakin farko, Lawan Yunusa Danzomo, da babban mai da shawara ga gwamna kan tsaro, Usman Muhammad Jahun, da babban sakataren gwamna, Muhammad Garun Gabas.

Kamun hukumar Hisbah

Ranar Juma'ar nan ne hukumar Hisbah a jihar Kano da ke maƙwabtaka da jihar Jigawa, ta tabbatar da kama Sankara da tsare shi a wani kango tare da matar aure.

Babban Daraktan hukumar Hisbah, Dr Abba Sufi ya bayyana cewa an kama kwamishina Sankara bayan wani ƙorafi daga ƙanin mijin wata mata, inda ya zarge shi da abin kunya.

Dr Sufi ya ce kwamishinan zai fuskanci caji a kotu kan zarge-zarge ciki har da samar da cibiyoyin sayar da ƙwaya mai suna Picklock da 360.

Musanta zargi

Rahotannin wasu jaridun ƙasar sun ce a jiya Juma'a, kwamishinan Auwal Danladi Sankara ya musanta zargin da aka yi masa na haramtacciyar mu'amala da matar aure, inda ya ce zargin ba shi da tushe, kuma ƙarya ce da aka yi don ɓata sunansa.

“A matsayina na magidanci, ina martaba aure kuma ba zan taɓa aikata abin da zai keta darajar aure ba,” in ji Auwalu Sankara, inda kuma ya sha alwashin ɗaukar matakin shari'a kan waɗanda suka yaɗa batun.

TRT Afrika