Gwamnatin Nijeriya ta umarci Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta ƙasar (NCAA) ta gudanar da cikakken bincike kan dukkan kamfanonin jiragen sama a ƙasar.
Ta ɗauki matakin ne kwanaki kaɗan da dakatar da kamfanin jirgin sama na Dana Air a ƙasar bayan wani jirginsa mai lamba 5NBKI ya kauce hanyarsa lokacin da ya sauka a a filin jirgin saman Murtala Muhammad da ke jihar Legas.
Ministan Ma'aikatar Sufurin jiragen sama na Nijeriya Fetus Keyamo ya shaida wa gidan talbijin na Channels TV cewa bayan matakin dakatar da kamfanin Dana Air da kuma bincikensa da ake yi, ''za a kuma gudanar da cikakken bincike kan dukkan kamfanonin jiragen sama da ke ƙasar domin tabbatar da tsaron lafiyar fasinjoji da lafiyar masana’antar sufurin jiragen sama ta Nijeriya".
Dakatarwar
A ranar Laraba da ta gabata ne, Keyamo ya umarci hukumar NCAA ta dakatar da kamfanin jirgin Dana, yana mai cewa hatsarin jirgin kamfanin na baya-bayan nan ya haifar da fargaba game da tsaron lafiyar fasinjoji da ayyukan ma'aikatar.
An dakatar da ayyukan kamfanin har sai an kammala gudanar da cikakken bincike, in ji Keyamo, kamar yadda ya umarci Darakta Janar na NCAA Chris Najomo ya aiwatar da matakin nan-take.
Hukumomi sun dakatar da kamfanin Dana Air ne awanni 24 da faruwar hatsarin ɗaya daga cikin jiragensa.
Sai dai a sanarwar da kamfanin ya fitar ya bayyana cewa babu wani fasinja da ya jikkata ko ya rasu sakamakon abin da ya faru.