Gwamnatin jihar Neja ta ce an mika wa hukumomin tsaro rahoto kan mai wa'azin don ci gaba da gudanar da bincike. / Hoto: Intsagram/mohammedumarubago

Hukumar Kula da Addinai ta jihar Neja ta dakatar da wani mai wa’azi a Suleja Muhammad Bin Muhammad tare da rufe makarantarsa saboda zargin yaɗa aƙidun ‘Boko Haram’.

Darakta Janar na hukumar Dokta Umar Farouk Abdullahi ya tabbatar wa TRT Afirka Hausa cewa an ɗauki matakin ne bayan zaman da malamai suka yi da shi suka gano cewa bai yi karatun addini ba.

Dakta Abdullahi ya ce hukumar ta Kula Addinai ba ta gamsu da yadda Muhammad Bin Muhammad yake gabatar da wa’azi ba, don haka aka gayyace shi domin tattaunawa da shi kan irin abubuwan da yake yaɗawa.

“An kunna masa bidiyo da dama na karatuttukansa, kuma ya tabbatar da cewa shi ne,” a cewar Dokta Abdullahi, inda ya ƙara da cewa daga nan ne aka fara yi masa tambayoyi a kan karantarwar tasa.

“Mun ɗauki fiye da awa biyu muna tattaunawa da shi, sai muka lura da matsalolinsa.”

Daraktan ya ce matsala ta farko da kwamitin malaman ya gano bayan tattaunawar ita ce, “bai yi karatu ba. Karatun addinin ma bai san shi ba”.

Matsala ta biyu a cewar Dokta Abdullahi ita ce abubuwan da yake karantarwa “gurɓatattun aƙidu ne, waɗanda suka yi kama da aƙidun Boko Haram, ba ma suka yi kama ba, aƙidun Boko Haram ne, domin shi ya soke karatun (certificate) shaidar karatu”.

Matsala ta uku kuma ita ce duk malaman kasar nan ya kafirta su, a cewar daraktan.

Matsala ta huɗu da aka gano daga karantarwarsa ita ce rashin yarda da kowace ƙungiya.

Matsala ta biyar ita ce ƙudurce cewa shiga gwamnati da dimukuradiyya da yin zaɓe duka kafirci ne, don haka dole a ƙaurace musu, kamar yadda hukumar ta addinai ta jihar Neja ta gano.

Matakan da aka ɗauka

Bayan tattaunawar da aka yi da mai wa’azin na Suleja, hukumar ta tabbatar da cewa “a yanzu dai ƙyale shi akwai hadari. Idan aka ƙyale shi fitina ta ƙullu a mazauninsa, to za ta ci Nijeriya,” a cewar Dokta Abdullahi.

Don haka ne kwamitin ya yanke hukuncin cewa “a yanzu dai a dakatar da shi daga dukkan wani wa’azi, makarantar Islamiyya kuma da yake yi a rufe makarantar,” in ji daraktan na hukumar addinai ta jihar Neja.

Hukumar ta ce za ta miƙa wa jami’an tsaro rahoto su yi bincike. Idan sun gamsu aƙidarsa ba ta da hatsari, za a ƙyale shi ya ci gaba da wa’azi, kuma a buɗe makarantarsa.

Ya ƙara da cewa dakatarwar da aka yi wa mai wa’azin ta shafi har a kafofin sada zumunta.

“Amma yanzu bisa tattaunawar da muka yi da shi, da kuma fahimta da muka yi wa addinin Musulunci, tsarinsa da yake kai da aƙidarsa Boko Haram ce,” a cewar Dokta Abdullahi.

Daraktan ya ce ba a kama mai wa’azin ba, kuma dakatarwar da aka yi masa ta wucin gadi ce, har zuwa lokacin da jami’an tsaro suka kammala bincike.

TRT Afrika da abokan hulda