Badaru da Matawalle tsofaffin gwamnoni ne da wasu ke gani ba su kawo ci-gaba sosai a jihohinsu ba./OTHER

An ambaci sunan tsohon gwamnan Jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubakar fiye da sau fiye da 20,000 a shafin Facebook tun bayan da aka sanar da cewa shi Shugaba Bola Tinubu ya bai wa Babban Ministan Tsaron Nijeriya.

Yayin da a shafin X wato tsohon Twitter kuwa an fi tattaunawa kan tsohon gwamnan Zamfara Mohammed Bello Matawalle, wanda shi ne karamin Ministan Tsaro da za su yi aiki a ma’aikata daya da Badaru.

A shekarun baya-bayan, rashin tsaro ya zama babban kalubalen da ake fama da shi a sassan daban-daban na Nijeriya, shi ya sa ma 'yan kasar ke zuba wa kowace gwamnati idanu a yayin nade-naden mukaman da suka shafi tsaro don ganin ko za a saka mutanen da suka dace.

Nada tsofaffin gwamnoni biyu daga jihohin Arewa Maso Yammacin Nijeriya a matsayin babba da karamin Ministocin Tsaro wani babban al’amari ne da ya dasa ayoyin tambaya da dama a zukatan ‘yan kasar da har ya sa suke ta sharhi.

Nijeriya na fama da matsalolin tsaro a sassa daban-daban. Hoto: Reuters

Shin an ajiye kwarya a gurbinta ne a wannan nadi? Wace irin rawa za su taka? Wadannan su ne wasu daga cikin abubuwan da wannan makala za ta yi nazari a kai.

Masu sharhi na ganin wannan nadi da Shugaba Tinubu ya yi wa Badaru da Matawalle kamar ya ci gaba ne daga inda tsohon shugaban kasar Muhammadu Buhari ya tsaya.

A zamanin mulkin Shugaba Buharin mukamin Ministan Tsaro ma dan arewacin kasar Janar Bashir Magashi ne ya rike shi, lamarin da wasu masana suka ce bai taimaka wa Arewa ba. Sai dai a lokacin Buhari minista daya aka yi ba babba da karami ba kamar na yanzu.

“A karkashin Shugaba Buhari kusan kashi 80 cikin 100 na mace-macen da aka samu na matsalar tsaro duk ‘yan arewa ne, don haka ba lallai yanzu ma hakan ta sauya zani ba,” a cewar Dr Kabiru Adamu, kwararre da ke sharhi kan sha'anin tsaro a Yammacin Afirka.

Labarin da za ku so ku karanta: Takaddama ta barke tsakanin jami'an tsaro da tsohon gwamnan Jihar Zamfara

Wani abu da masu tattaunawa a shafukan sada zumunta ke kara fada kan mukaman tsoffin gwamnonin shi ne duba kan ko sun taka wata rawar gani don shawo kan matsalolin tsaro a jihohinsu a lokacin da suke mulki.

Dr Adamu, wanda kuma shi ne shugaban kamfanin Beacon Security Consulting mai bin diddigin harkokin tsaro a Nijeriya, ya ce Jihar Kano da makwabciyarta Jihar Jigawa inda Badaru ya yi mulki tsawon shekara takwas su ne ba su fuskanci kalubalen tsaro ba a kusan duk jihohin arewa maso yammacin kasar.

Jihar Zamfara ta sha fama da matsalar tsaro, ciki har da sace 'yan matan wata sakandare da aka yi lokacin Bello Matawalle. Hoto: AA

“Amma wannan kuma ba saboda abin da ya yi ne ko wanda bai yi ba, yanayi ne ya taimaka masa. A takaice dai ba mu ga wani matakai ko tsare-tsare da shi (Badaru) ya fito da su ba da za a ce su suka taimaka wajen ingantuwar tsaro a jihar.

Sabon karamin Ministan Tsaron kuwa Bello Matawalle, jiharsa ta Zamfara ta yi kaurin suna wajen fama da matsalar tsaro da hare-haren inda daruruwan mutane suka rasa rayukansu, duk da cewa dai za a iya cewa shi ma gadar hakan ya yi.

A tattaunawar ‘yan Nijeriya, wasu na ganin watakila zai iya taka wata rawa ta magance wata matsalar tsaron kasar musamman ta hanyar yin sulhu da ‘yan bindiga, amma ga wasu da dama kuma ciki har da masana, suna ganin “gara wata wainar ma a kan ta gero.”

“Shi kam Bello Matawalle abin nasa ma ya fi muni dangane da matsalar tsaro da aka samu a jiharsa saboda babu jihar da matsalar tsaro ta fi ta’azzara irin tasa,” in ji Dr Adamu.

“Maganar gaskiya dukkan su biyun ban ga alamar an ajiye kwarya a gurbinta ba,” masanin ya kara da cewa.

Wata tambayar da ‘yan Nijeriya ke yi a tattaunawarsu ta intanet ita ce ko kujerar ministan tsaro ta fi dacewa da wanda ya taba saka kaki ne ko kuwa za a iya bai wa kowa rikonta?

Tsohon gwaman jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar, ya ce daga harkar kasuwanci ya shiga siyasa. Hoto/Facebook/Muhammad Abubakar Badaru

Kabiru Adamu ya ce ba lallai sai wanda ya taba rike mukami na fannin tsaro ba ne zai rike mukamin, ko dan siyasa irin su Badaru da Matawalle za su iya, “amma dai za a fi son a bai wa wanda ya taba aikin tsaro don zai fi sanin kan lamarin.”

Shawarwari ga sabbin ministocin tsaro

Mai sharhi kan tsaron wanda ya sha fitar da sakamakon bincike da kididdiga na ayyukan tsaro da ke faruwa a Nijeriya, wanda kuma ya shafe sama da shekara 20 yana wannan aiki, Kabiru Adamu ya ba da wasu shawarwari da ya ce idan sabbin ministocin tsaron suka bi za su yi musu amfani.

  • Su samu masana tsaro don su dinga ba su shawara da kuma yin aiki da su
  • Dama aikin minista shi ne tabbatar da cimma burin da ake so a cimma, ba kai za ka yi aikin da kanka ba, don haka abu mafi kyau shi ne su nemi mataimaka da suka san abin da suke yi
  • Su tsaya su karanci jadawalin da gwamnatin tasu ta fitar a lokacin yakin neman zabe, a ciki akwai abu bakwai da ta saka a ciki da take son cimma a fannin tsaro, sai su yi nazarinsu
  • Su samu hadin kai a tsakaninsu da junansu da kuma ministocin harkokin cikin gida da na sha’anin ‘yan sanda
  • Su fahimci yadda za su yi aiki da majalisa, ita majalisa ita ke da alhakin inganta dokoki da duba yadda bangaren zartarwa ke tafiya, hadin kai a tsakaninsu zai yi kyau
  • Su samu wani tsohon soja kuma babba wanda yake da kwarewa ake kuma jin maganarsa don ya dinga saka su a hanya, musamman wanda manyan hafsoshin tsaro ke jin maganarsa.

TRT Afrika