Hukumomi a Jihar Neja da ke tsakiyar Nijeriya sun tabbatar da mutuwar gomman mutane sakamakon ruftawar wata mahaƙar ma'adinai a yankin ƙaramar Hukumar Shiroro.
Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa na Jihar Neja, Abdullahi Baba Arah ya shaida wa manema labarai cewa lamarin ya auku ne ranar Litinin, kuma ya ce mutane da dama sun mutu ko da yake bai bayyana adadinsu ba.
Amma ganau sun ce mutum aƙalla 50 sun mutu yayin da gommai suka jikkata bayan ƙasa ta rufta da su a yayin da suke haƙar ma'adinai a ƙauyen Farin Doki da ke yankin Eran na Shiroro.
Abdullahi Baba Arah ya ce tuni suka kai jami'ansu domin kai ɗaukin gaggawa, yana mai cewa an garzaya da waɗanda suka jikkata asibitin da ke yankin.
"Bayan sa'o'i biyar da ruftawar mahaƙar an samu damar zaƙulo mutane shida da ransu amma suna cikin mawuyacin yanayi,'' in ji Abdullahi Yarima, wanda lamarin ya faru a kan idanunsa, kuma tsohon shugaban ƙaramar hukumar Shiroro.
Yarima ya ƙara da cewa, "daga cikin mutanen da iftila'in ya rutsa da su har da shugaban da ke sa ido a aikin haƙar ma'adinan inda aka kwashe sama da shekara goma ana hakar zinari."
Gwamnatin Nijeriya ta haramta haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba, lamarin da ta ce yana haddasa rasa rayuka da yin illa ga tattalin arzikin ƙasar.
Shugaba Bola Tinubu ya sha alwashin bunƙasa fannin ma'adinan Nijeriya domin samun kuɗaɗen-shiga da rage dogaro da man fetur, yana mai cewa a halin da ake ciki wannan fanni ba ya samar da sama da kashi ɗaya na kuɗin-shigar ta.
A kwanakin baya ne Ma'aikatar Harkokin Ma'adinai ta Nijeriya ta gudanar da garambawul inda ta amince ta bai wa masu zuba jari kashi 75 na hannun-jarin kamfanin haƙar ma'adinai na ƙasar, tare da hana fitar da ma'adinan da ba a sarrafa ba.