Ana fargabar cewa mutane da yawa sun mutu bayan wata tankar mai ta yi hatsari abin da ya sa motoci da dama suka kama da wuta a jihar Rivers da ke kudancin Nijeriya.
Lamarin ya faru ne ranar Juma'a da daddare a kan hanyar East-West Road da ke yankin Eleme, wadda ta daɗe da lalacewa lamarin da ya jefa masu bin ta cikin hatsari.
Gidan talbijin na Channels TV ya ruwaito cewa hatsarin ya faru ne yayin da wata mota ta ci karo da tankar man a daidai lokacin da take ƙoƙarin kauce wa ramukan da suka ciki titin, kuma nan-take tankar man da motoci da yawa suka kama da wuta.
Bayanai sun ce mutanen da ba a kai ga tantance adadin su ba sun mutu bayan sun kasa fita daga motocin da suke ciki.
Bidiyoyi da hotunan da aka riƙa wallafawa a soshiyal midiya sun nuna yadda motoci da dama, ciki har da manyan motocin ɗaukar kaya, suke ci da wuta.
Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, wanda ya je wurin da hatsarin ya faru ranar Asabar, ya ce "abin da nake gani yanzu shi ne, motoci da dama sun ƙone sannan an rasa rayuwa" ko da yake bai faɗi adadin asarar da aka yi ba.
"Na umarci jami'an tsaro su ba mu cikakken bayani game da lamarin...Dukkanmu mun san halin da wannan hanya take ciki. Wannan abin takaici ne matuƙa," in ji Gwamna Fubara.
Hanyar ta East-West mallakin gwamnatin tarayyar Nijeriya ce, wadda hukumomi suka sha alwashin gyarawa amma hakan ya gagara.