Masu aikin ceto a Nijeriya na ci gaba da neman mutanen da suka ji rauni bayan wata fashewa da ta faru a birnin Ibadan na Jihar Oyo a ranar Talata da daddare, lamarin da ya jijjiga gidaje tare da tsoratar da mutane har suka bazama kan tituna.
Gwamnan jihar Seyi Makinde ya ce binciken wucin gadi ya nuna cewa masu hakar ma'adinai ne suka ajiye ababen fashewa a cikin wani gida wanda hakan ya jawo fashwar.
An ji karar fashewar a birnin Legas mai nisan kilomita 30 daga Ibadan. Wasu mazauna yankin sun ce ƙarfin fashewar ta sa tagogin gidajensu sun yi rugu-rugu
“Hukumomin da abin ya shafa suna gudanar da aikin bincike da ceto a wurin da lamarin ya faru, an yi kira ga mazauna jihar da su kwantar da hankalinsu saboda gwamnatin jihar Oyo na kan gaba wajen shawo kan lamarin,” in ji jihar Oyo a wata sanarwa da ta fitar.
Tun da fari, Kwamishinan watsa labarai na jihar Prince Dotun Oyelade ya ce "mazaunan Ibadan da kewaye sun ki ƙarar fashewar wani abu da ba a saba gani ba da misalin karfe 8 na dare (1900 GMT) da yammacin yau."
'Mutum bakwai sun rasu, 77 sun samu rauni'
Sai dai a sanarwar da gwamnan jihar Seyi Makinde ya fitar, gwamnan ya jajanta wa wadanda wannnan lamarin ya faru da su bayan ya kai ziyara inda ya tabbatar da cewa akai mutum biyu wadanda suka rasu sannan 77 sun samu rauni.
Haka kuma gwamnan ya ce ya bayar da umarni a biya kudin asibiti na wadanda lamarin ya shafa da kuma ba su matsuguni na wucin gadi da kuma tabbatar da cewa an taimaka musu sun sake gina rayuwarsu.
Gwamnan ya bayyana cewa duk wasu wadanda aka kama da hannu a wannan lamarin za su yaba wa aya zakinta.