Ƴan sanda a Kamaru sun kama wani matashi da laifin shan jini da ya cin naman wani yaro. Hoto: Getty

'Yan sanda a Kamaru sun kama wani matashi a garin Mbouda da ya kusan aika wani jariri lahira bayan cizonsa da kuma cin naman kumatun yaron.

An miƙa matashin mai suna Tchinda mai shekara 20 ga jami’an tsaro bisa laifin cizo da kuma cin naman yaron ɗan shekara ɗaya da haihuwa.

Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi a ƙauyen Bamessingue da ke yankin Mbouda a yammacin ƙasar Kamaru.

A wani faifan bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta, Tchinda ya bayyana cewa ya aikata laifin ne sakamakon mawuyacin yanayi da ya shiga na buƙatar shan jinin ɗan'adam.

Yana mai cewa ''na aikata hakan ne don na iya ceton rayuwata,'' bayan nan ya yanke shawarar cizon yaron sau biyu a kumatu da kuma ciki, sannan ya cinye naman. kamar yadda kafar yaɗa labarai ta Kamaru, CNA ta rawaito.

"Ba zan sake cin naman yara ba, a taimaka a kuɓutar da ni, ku kwance ni, ba zan gudu ba," a cewar Tchinda yayin da yake kokawa a hannun ƴan sanda.

“Suna ƙoƙarin ɗauke ni" in ji shi.

''Na zo ga yayana ina yi masa bayanin halin da na tsinci kaina a ciki don ya taimaka ya cece ni amma bai nuna damuwa akai ba," a cewar Tchinda.

Matashin ya ƙara da cewa ''Na shaida wa ɗan'uwana cewa ina cikin hatsari, ana neman na kawo jinin ɗan'adam ko a kashe ni.''

Bayan yin kunnen ƙashi da rashin kulawa da Tchinda ya samu daga wajen ɗan'uwansa, sai aka yi rashin sa'a akwai ƙaramin yaro a gidan, wanda ya afkawa don biyan bukatarsa ta shan jini.

An dai yi ƙoƙarin ceto yaron bayan kawo masa ɗauki da al'ummar gari suka yi, kuma tuni aka garzaya da shi aisibiti don samun kulawa.

Tuni dai jami'an ƴan sanda suka shiga bincike kan lamarin tare da ba da tabbacin samar wa yaron adalci.

TRT Afrika