Daga karshen watan Afrilu kasar Kamaru za ta fara ba da izinin shiga kasar ta intanet wato evisa a Turance.
Wata sanarwar da Ma’aikatar Harkokin Wajen kasar ta fitar ta ce ta dauki matakin ne don jan hankalin matafiya zuwa kasar.
“Ministan Hakokin Wajen kamaru, Mbella Mbella yana amfani da wannan damar ya sanar da mutane na gida da ketare cewar daga ranar 30 ga watan Afrilu dukkan bukatar neman shiga kasar za a rinka cikawa ne a intanet ta www.evisacam.cm,” in ji sanarwar.
Ta kara da cewa hatta da mika takardar neman izinin shiga da kuma biyan kudin neman izinin shiga kasar za a rinka yi ne ta hanyar intanet.
Ba da jimawa ba za a saka tsarin evisa din a iyakokin kasar na ruwa da na kasa, in ji sanarwar.
TRT Afrika da abokan hulda