Manufar taron, wanda Ƙungiyar Ƴan Jarida ta Afirka ta shirya, ita ce duba shirin da kafofin watsa labaran Afirka ke yi wajen amfani da fasahar AI, da fito da tsare-tsare da shawarwari ta yadda za a yi amfani da fasahar yadda ya dace / Hoto: Reuters

An fara gudanar da wani taro kan kafofin watsa labaran Afirka da ƙirƙirarriyar basira (AI) a babban birnin Kamaru, Yaounde.

"Dole ne kafofin watsa labarai su sauya, su ribaci ƙirƙirarriyar fasahar AI sannan su bunƙasa al'adun Afirka," a cewar Ministan Sadarwa na ƙasar Rene Emmanuel Sadi, yayin buɗe taron a babban zauren Congress Palace ranar Litinin.

Manufar taron, wanda Ƙungiyar Ƴan Jarida ta Afirka ta shirya, ita ce duba shirin da kafofin watsa labaran Afirka ke yi wajen amfani da fasahar AI, da fito da tsare-tsare da shawarwari ta yadda za a yi amfani da fasahar yadda ya dace, da haɗa kai tsakanin ƴan jarida da kuma fito da manufa ta bai-ɗaya ta amfani da fasahar AI a Afirka.

Ginshiƙai

Ministar Watsa Labarai da Fasahar Sadarwa na Gabon mai maƙwataka Laurence Ndong ta yi maraba da shawarar da Hukumar Ilimi da Fasaha da Al'adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya UNESCO ta bayar kan bin tsarin da ya kamata wajen amfani da ƙirƙirarriyar fasaha.

Ta yi ƙarin bayani kan irin tasirin da fasaha ke yi a wajen aikin jarida.

"Fasahar AI a fagen aikin jarida ta wuce bankaɗo labaran ƙarya. Akwai wasu manhajoji da a yau za su mayar da aikin jarida mai sauƙi," kamar yadda take cewa.

Ranar farko ta taron mai taken "Sabuwar fuskar Kafofin Watsa Labaran Afirka: Ƙirƙirarriyar Basira ta AI" ta samu halartar ƙwararru a fannin aikin jarida, da masana, da ƴan siyasa, da ƴan jarida da kuma ƴan ƙungiyoyin al'umma.

TRT Afrika