Rundunar ƴan sandan ta ce a yanzu haka waɗanda ake zargin suna hannunta. Hoto: NPF

Rundunar ƴan sandan Nijeriya ta ce ta kama wasu mutum biyu, ciki har da wani Shugaban Ƙaramar Hukumar Jihar Binuwai da ake zargi da hannu a yunƙurin kashe Kakakin Majalisar Dokokin jihar.

“Daga cikin waɗanda aka kama har da Shugaban ɗaya daga cikin Ƙananan Hukumomin Jihar Binuwai,” kamar yadda sanarwar rundunar ƴan sandan ta ƙasa mai ɗauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a ACP Olumuyiwa Adejobi, ta faɗa.

Sanarwar ta ƙara da cewa binciken farko ya bayyana cewa ana zargin Shugaban Ƙaramar Hukumar da haɗa baki da wani ɓata gari da nufin kashe Kakakin Majalisar Dokokin Jihar ta Binuwai, Honorabul Aondona Hycenth Dajoh.

“Ba tare da ɓata lokaci ba sai jami’an sashen Leƙen Asiri da Tawagar Gaggawa ta Leƙen Asiri suka yi abin da ya dace bayan samun bayanan sirri a kan shirin yunƙurin kisan kan.”

Rundunar ƴan sandan ta ce a yanzu haka waɗanda ake zargin suna hannunta, kuma suna bayar da haɗin kan da ya dace wajen gudanar da binciken da ake yi.

Ƴan sanda sun kuma tabbatar da cewa waɗanda ake zargin za su fuskanci shari’a idan aka tabbatar da laifinsu.

Kazalika rundunar ta nanata wa ƴan Nijeriya cewa ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen ba su kariya da kuma tabbatar da bin doka da oda a kowane mataki.

TRT Afrika