Wannan ne karo na uku da Côte d'Ivoire ta ɗauki kofin nahiyar Afirka./Hoto:Reuters

Ƙasar Côte d’Ivoire ta yi nasarar ɗaukar kofin nahiyar Afirka bayan ta doke Nijeriya da ci 2-1 a wasan ƙarshe da suka fafata ranar Lahadi a filin wasa na Alassane Ouattara da ke Abidjan, babban birnin ƙasar.

Tawagar Super Eagles ce ta soma cin ƙwallo ta hannun William Troost-Ekong gabanin a tafi hutun rabin lokaci inda ya doka ƙwallon da ka a ragar the Elephants.

Sai dai ɗan wasan Côte d’Ivoire Franck Kessie ya farke ƙwallon jim kaɗan bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.

Daga nan ne fa ƴan wasan Côte d’Ivoire suka matsa wajen kai hari a gidan Nijeriya har lokacin da Sebastien Haller ya zura ƙwallo a ragar Super Eagles saura minti tara a kammala wasa.

Wannan ne karo na uku da Côte d'Ivoire ta ɗauki kofin nahiyar Afirka.

Côte d'Ivoire ta soma gasar da ƙafar-hagu inda ta sha kashi sau biyu a matakin rukuni, ciki har da wulaƙancin da Equatorial Guinea ta yi mata a ci 4-0. Amma daga bisani tawagar ƙwallon ƙafar ƙasar ta zage dantse har ta kai wannan mataki.

TRT Afrika