Rundunar 'yan sandan Jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Nijeriya ta ce ta kama mutum hudu bisa zargin su da hannu a mutuwar wani matashi da aka zarge shi da satar waya.
A ranar Laraba ne matashin mai suna Abdullahi Abba ya rasu bayan zargin da iyayensa suka yi cewa jami'an tsaro sun azabtar da shi bisa zarginsa da satar waya.
Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar SP Suleiman Nguroje ya shaida wa TRT Afirka cewa uku daga cikin mutum hudu da aka kama 'yan sanda ne, dayan kuma farar-hula, wanda kuma shi ne ya zargi Abdullahi da satar wayar.
"Tuni muka kaddamar da bincike kuma har mun kama 'yan sanda masu mukamin insifekta biyu da kofur daya da kuma mutumin da aka ce shi ya zargi yaron da satar wayar. A yanzu haka suna sashen binciken manyan laifuka na hukumarmu," in ji shi.
Mahaifin Abdallah mai suna Dr Tukur Abba ya shaida wa TRT Afrika cewa sun yi maraba da wannan mataki na rundunar 'yan sanda, amma duk da haka za su ci gaba da bibiyar lamarin har sai sun tabbatar an yi wa dansu adalci.
Rundunar 'yan sandan ta ce tana ci gaba da bincike karkashin hadin gwiwa da rundunar sojoji don kara gano masu hannu a lamarin tare da daukar matakin da ya dace.
Me ya faru tun farko?
A ranar Asabar din makon jiya ne rahotanni suka ce wani makwabcin su Abdullahi ya zarge shi da sace masa wayarsa ya kuma kai batun gaban rundunar jami'an tsaro ta Operation Farauta, mai hadin gwiwar 'yan sanda da sojoji, wacce take kula da al'amuran da suka shafi satar mutane da fashi a fadin jihar.
Iyayen Abdullahi, dan shekara 17, wanda yake aji biyar a makarantar sakandare sun ce rundunar ta Operation Farauta ta dauke shi ta tafi da shi tare da azabtar da shi har ya fita hayyacinsa.
Sun kuma ce bayan mayar da shi gida ne sai ya fara aman jini inda aka garzaya da shi Asibitin Koyarwa na Modibbo Adama da ke Yola inda ya cika a can.
Wannan lamari ya harzuka mutane sosai a ciki da wajen jihar inda har aka kaddamar da maudu'in #JusticeForAbdallah na neman a yi wa Abdullahi adalci ta hanyar bi masa hakkinsa.
SP Nguroje ya ce rundunar 'yan sanda ba ta samu labarin ba sai bayan da aka mayar da shi gida daga hannun rundunar Operation Farauta aka kai shi asibiti cikin fitar hayyaci, sannan aka kai musu rahoton.
"Da aka kai shi asibiti ya fara amai ya fita daga hayyacinsa a lokacin ne lauyansu ya tuntubi kwamishinan 'yan sanda inda ba tare da bata lokaci ba shi kuma ya ba da umarnin a ba shi dukka kulawar da yake bukata don ceton lafiyarsa.
"Amma dai a yanzu dole mu jira zuwa lokacin da sakamakon binciken da muke yi tare da hadin gwiwar abokiyar aikinmu ta tsaro don gane hakikanin abin da ya faru," a cewar mai magana da yawun 'yan sandan.
A karshe ya ja hankalin al'ummar jihar da su kwantar da hankalunsa tare da ba su tabbacin cewa hukuma za ta yi abin da ya dace wajen bai wa kowa hakkinsa.
Me iyayen Abdallah suka ce?
A hirarsa da TRT Afrika, mahaifin Abdallah Dr Tukur ya ce sun shiga cikin damuwa da matukar tashin hankali kan abin da ya faru, kuma suna fatan hukumomi su bi wa dansu kadinsa.
Ya ce a ranar Asabar ne wani mutum da suke unguwa daya ya je gidan da mota da wani mai tuka ta da nufin cewa zai dauki Abdallah ya kai shi wajen hukuma don a thume shi ya fito da wayar da wani yaro da ake zargin shi ya sata ya ce ya bai wa Abdallan.
Ya ce ya yi kokarin fahimtar da su cewa sai ya ga jami'an tsaro amma suka nuna masa ai ba komai za a je a dawo ne kawai.
"Bayan awanni sai ga su tare da wasu jami'an tsaro sun dawo da Abdallah a jigace ya fita hayyacinsa saboda dukan azaba da ya sha.
"Haka muka kwashe shi muka yi asibiti aka yi masa gwaje-gwaje ciki har da hoton illahirin jiki wato CT Scan, tun ranar Asabar muke fama har ranar Laraba da Allah Ya yi ikonsa ya cika," a cewar Dr Tukur.
Mahaifin marigayin ya sha alwashin cewa za su tsaya tukuru don ganin an bi musu hakkin ran dansu.