Hezbollah ta bayyana ranar Alhamis cewa ta ƙaddamar da ayyukan soji 24 cikin sa’o’i 24 kan dakarun Isra’ila da motocin soji da wuraren da suke a faɗin kudancin Lebanon.
Ƙungiyar ta kuma ce hare-haren sun haɗa da na jirage mara matuƙa da ruwan makamai masu linzami a matsayin martani ga yadda Isra’ilka ke ci gaba da saɓa wa yarjejeniyar tsagaita wuta kan garuruwa na fararen hula .
A cikin wasu jerin sanarwa, ƙungiyar ta bayyana cewa wasu hare-jaren sun mayar da hankali ne kan garin Haddatha, inda mayaƙanta suka yi arangama da dakarun Isra’ila da ke tahowa da kuma wani ɓangare na masu motoci masu sulke a ɗaya daga cikin arangama mafi muni a cikin ‘yan kwanankin nan.
Hezbollah ta bayyana cewa, hare-haren jirage mara matuƙa akai-akai sun mayar da hankali ne kan wuraren da sojin Isra’ila suka fi yawa, yayin da aka kai hari kan aƙalla tankokin yaƙi samfurin Merkava huɗu da buldoza biyu samfurin D9 a samame daban daban .
Ƙungiyar ta kuma ce mayaƙanta sun yi arangama da dakarun Isra’ila da ke dannawa Haddatha tare da kai hari kan waɗanda ke mara musu baya da manyan bindigogi da rokoki na kusan mintuna 30.
Ta ƙara da cewa ta kai hari kan wani jirgi mara matuƙi na Isra’ila samfurin Hermes 450 a ɓangaren tsakiya da wani makami mai linzami da ake harbawa sama.
A ranar Laraba , sojin Isra’ila ta ba da sanarwar cewa bakwai daga cikin sojojinta, ciki har da hafsoshi biyu, sun ji rauni bayan wani jirgi mara matuƙi mai ɗauke da bam ya faɗi a kudancin Lebanon.
Sojin ta ce wata soja mace ta ji rauni sosai yayin da hafsoshi biyu da sojoji biyu suka ji matsakaicin raunuka. Ƙarin sojoji biyu sun ji rauni kaɗan.
Hare-haren Isra’ila a faɗin Lebanon sun ci gaba duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da Amurka ta samar wadda ta fara aiki a hukumance ranar 17 ga watan Afrilu kuma daga baya aka tsawaita ta zuwa farkon watan Juli.
Tun ranar 2 ga watan Maris , Isra’ila ta fara kai hare-hare masu yawa kan Lebanon inda ta kashe mutum 3,073, ta jikkata wasu 9,362 tare da raba mutum fiye da miliyan 1.6 (kimanin kashi ɗaya cikin biyar na ƙasar) da gidajensu, in ji jami’an Lebanon.












