| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Ɗalibai 16 sun rasu sakamakon gobara a wata makarantar 'yanmata a Kenya
Masu bincike sun gudanar da tsauraran tambayoyi ga ɗalibai da malamai, sannan kuma sun duba hotunan kyamarorin CCTV.
Ɗalibai 16 sun rasu sakamakon gobara a wata makarantar 'yanmata a Kenya
Ɗalibai 16 sun rasu sakamakon gobara a wata makarantar 'yanmata a Kenya / Reuters

’Yan sanda a Kenya sun ce an kama dalibai takwas kan zargin kona wata makarantar 'yan mata, wani abin da ya yi sanadiyyar mutuwar yara 16 da kuma jikata wasu 79.

Wutar ta tashi a safiyar ranar Alhamis a Makaranatr ‘Yanmata ta Utumishi Girls Academy a gundumar Nakuru, kusan kilomita 120 (miles 75) arewacin babban birnin Nairobi.

“Binciken farko ya gano ɗalibai takwas a matsayin waɗanda ake zargi da hannu ko kuma masu alaƙa da shirin da aiwatar da wannan harin ƙona makaranta,” in ji daraktan binciken manyan laifuka a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.

An bayyana cewa saman bene na ginin mai hawa biyu, wanda ke da ɗakuna 12 da ke ɗauke da gadaje 135 masu hawa ya samu mummunar barna sosai, a cewar ‘yansanda.

An tattara shaidun binciken kimiyya na laifi da aka samu a wurin

Masu bincike sun gudanar da tsauraran tambayoyi ga ɗalibai da malamai, tare da duba bidiyon CCTV da sauran shaidun binciken kimiyya (forensic evidence) domin gano musabbabin gobarar — wadda har yanzu ba a tabbatar da dalilinta ba.

An bayyana cewa makarantar na da alaƙa da Sashen ‘Yan Sandan Ƙasa (National Police Service), kuma yawancin ɗalibanta ‘ya’yan jami’an ‘yansanda ne.

‘Yan sanda sun ce an gano gawawwaki 16 gaba ɗaya, kuma an kai su ɗakin ajiye gawarwaki (mortuary) domin tantance su.

Iyayen da suka firgita sun taru a makarantar bayan labarin wutar ya yadu a ranar Alhamis, kuma zuwa maraice wasu har yanzu ba su san makomar 'ya'yansu ba.

Tarihin gobarar makarantu

An sha samun gobarar makarantu masu muni a Kenya, inda tsarin makarantun kwana ya zama ruwan dare a matsayin abin da aka gada zamanin mulkin mallaka na mishan da Biritaniya.

A baya an zargi yara da gangan haddasa wasu daga cikin waɗannan gobarar. Wani rahoto ya nuna an samu shari'o'in ƙone-ƙone 63 a makarantu a shekarar 2018 kadai.

An zargi ɗalibai bayan gobarar ɗakin kwana a shekarar 2001 a gundumar Machakos a kudu, wacce ta kashe mutane 67.

Gobarar ɗakin kwana a 2024 a Hillside Endarasha Academy a gundumar Nyeri ta kashe samari 21, abin da ya tilasta wa gwamnati yin alkawarin gudanar da binciken tsaro a duk makarantu da gurfanar da masu laifi — duk da haka ba a tabbatar ko an aiwatar da waɗannan matakan ba.

A ranar Alhamis, Ministan Ilimi ya ce ma'aikatar ta rufe kusan makarantu 350 tun daga 2024 saboda rashin bin ka'idojin tsaro.