Aƙalla mutane 50 ne suka mutu yayin da aka yi garkuwa da mata da yara da dama a wani hari da aka kai wani ƙauye a Jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Nijeriya.
Harin, wanda ‘yan ta’adda da ake kira ‘yan bindiga a yankin suka kai, ya fara ne a daren Alhamis kuma ya ci gaba har zuwa safiyar Juma’a. Maharan da suka iso a kan babura sun banka wa gine-gine wuta tare da harbin mazauna ƙauyen Tungan Dutse da suka yi ƙoƙarin tserewa, kamar yadda Hamisu Faru, ɗan majalisar jiha, ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu a ranar Asabar.
“Tun daga daren Alhamis har zuwa safiyar yau babu wanda ya samu barci. Wasu mutane sun rasa ‘yan uwa uku daga cikin iyalansu,” in ji Faru ga Anadolu.
An shirya gawawwakin waɗanda suka mutu domin jana’izar gama-gari, inda aka lulluɓe su da farin likkafani a ranar Asabar. Har yanzu ba a tantance adadin mutanen da aka yi garkuwa da su ba, yayin da jami’an yankin ke ci gaba da ƙididdige waɗanda suka ɓace.
Halin tsaro a Nijeriya na ci gaba da taɓarɓarewa, musamman a yankin arewa maso yamma inda Jihar Zamfara take. Yankin ya daɗe yana fama da hare-haren ‘yanbindiga, sace-sace da kashe-kashe, lamarin da ya raba dubban mutane da muhallansu tare da jefa wasu da dama cikin haɗari.
Gwamnatin Nijeriya ta ɗauki wasu matakai domin magance matsalar, ciki har da tura sojoji da kuma haɗin gwiwa da ƙasashen waje kamar Amurka wajen samun tallafin fasaha da musayar bayanan sirri.
Sai dai har yanzu lamarin na ci gaba da kasancewa mai ƙalubale, sakamakon Ƙaruwar barazanar tsaro daga ƙungiyoyin ‘yan ta’adda.













