Jami’an asibitin sun ce akalla mace daya da yara biyu na daga cikin wadanda suka mutu. Hoto: AFP

1522 GMT — Wani hari ta sama da Isra'ila ta kai ya kashe akalla mutane 14, ciki har da yara biyu, a makarantar Majalisar Dinkin Duniya da ta zama matsugunin iyalan Falasdinawa da ke tsakiyar Gaza, in ji jami'an asibiti.

Jami'ai daga asibitin al-Awda da ke Nuseirat sun ce sun karbi gawarwakin mutane 10 da harin ya kashe, sannan an kai wasu mutum hudu da suka mutu asibitin shahidan al-Aqsa da ke Deir al Balah.

Jami’an asibitin sun ce akalla mace daya da yara biyu na daga cikin wadanda suka mutu, sannan akalla mutane 18 sun samu raunuka.

More updates👇

1348 GMT — Adadin wadanda suka mutu a Gaza sakamakon harin da Isra'ila ta kai ya karu zuwa 41,084

Harin da sojojin Isra'ila suka kai a Gaza ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 41,084 tare da raunata 95,029 tun daga ranar 7 ga watan Oktoba, in ji ma'aikatar lafiya ta Falasdinu.

Akalla mutane 64 ne suka mutu a cikin sa'o'i 24 da suka gabata.

1256 GMT — Shugaban Iran ya caccaki Ƙasashen Yammacin duniya kan yakin Gaza da kuma goyon bayan Isra'ila

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya caccaki Kasashen Yammacin Duniya yana mai cewa Isra'ila na yin kisan kiyashi a yakin Gaza da kuma amfani da makaman Turai da Amurka wajen yin hakan.

Pezeshkian, wanda ya yi magana a Bagadaza a farkon ziyararsa ta farko a ketare tun bayan hawansa mulki, yana fatan karfafa alakar Tehran da Bagadaza a yayin da ake fama da rikici a yankin.

TRT World