Tun bayan naɗin sabon Sufeto Janar na ’yan sanda a Nijeriya wasu masana tsaro suka fara sharhi kan dimbin kalubalen da ke gabansa, musamman idan aka yi la’akari da tarin matsalolin tsaron da kasar take fama da su a halin yanzu.
Olatunji Rilwan Disu ya maye gurbin Kayode Egbetokun ne wanda ya yi murabus ranar Talata. A watan Yunin 2023 ne Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya naɗa Kayode Egbetokun a matsayin Sufeto Janar na ‘yansandan
An haifi sabon mukaddashin ’yan sandan ne a jihar Legas da ke kudu masu yammacin Nijeriya ranar 13 ga watan Afrilun 1966.
Ya shiga aikin ɗansanda ne a ranar 18 ga watan Mayun 1992, inda ake sa ran zai yi ritaya daga aiki a cikin wannan shekara saboda zai cika shekara 60 cif a duniya a cikin watan Afrilu mai zuwa. Ko da yake saboda gyarar da majalisar dokokin kasar ta yi wa dokar ’yansanda wato Police Act a watan Yulin shekarar 2024, yanzu sabon sufeto janar din zai iya kammala wa’adinsa na shekaru hudu, sai dai idan bisa radin kansa ya zabi ya yi murabus ko kuma shugaban kasa ya sauke shi daga kujerar.
Tunji Disu shi ne ya shugabanci sashen kai ɗauki da tattara bayanan sirri na rundunar ƴansandan kasar bayan sauke wanda ya gabace shi, Abba Kyari a shekarar 2021.
Babban kalubalen da sabon sufeto janar din ’yan sanda zai yi fama da shi ne batun tsaro wanda ya hada da matsalar satar mutane don neman kudin fansa da hare-haren ’yanfashin daji da matsalar Boko Haram da ISWAP da ta Lakurawa da rikicin makiyaya da manoma da sauransu.
A makonni uku na wannan wata an kashe fiye da mutum 330 a arewacin Nijeriya. Masana harkokin tsaro suna yawan cewa yana da wuya ka samu kasa wacce ba ta cikin yaki da za a rika kashe mutane barkatai haka.
Shugaban kamfanin tsaro na Beacon Consulting a Nijeriya kuma masanin kan al’amuran da suka shafi tsaro Dokta Kabiru Adamu ya taba shaida wa TRT Afrika Hausa cewa mutum fiye da 10,000 suka mutu a Nijeriya a shekarar 2025 sanadin matsalolin tsaron da kasar take fama da su.
Sannan wani kalubale da ke gaban sabon Sufeto Janar din ’yansandan shi ne inganta yanayin aikin ’yansanda ta hanyar bunkasa albashi da walwalarsu da kuma samar musu kayan aiki na zamani da suke bukata.
Inganta tsarin albashin ’yansanda yana da muhimmanci sosai saboda kamar yadda wasu masana suke fada, hakan zai taimaka wajen rage matsalar karbar cin hanci da rashawa ake yawan zarginsu da yi.
Kazalika wani abu da ya kamata sabon Sufeto Janar din ya ba muhimmanci shi ne batun tattara bayanan sirri da amfani da su wajen dakile barazanar tsaro kafin matala ta auku, kamar yadda masana tsaro suke yawan bayar da shawara.
Sannan batun daukar sabbin kananan ’yansanda 50,000 da Shugaba Bola Tinubu ya yi alkawari a watan Nuwamban bara lokacin da ya ayyana dokar ta-baci kan harkar tsaro a kasar, masana na ganin hanzarta yin hakan zai taimaka sosai wajen tunkarar matsalolin tsaron da kasar take fama da su a yanzu.













